Hamas ta ce ba zata shiga cikin zabe na gaba da wa´adi ba | Labarai | DW | 17.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas ta ce ba zata shiga cikin zabe na gaba da wa´adi ba

Kungiyar Hamas ta ce zata kauracewa zaben gaba da wa´adi da shugaba Mahmud Abbas ya ba da shawarar gudanarwa. FM Isma´il Haniyah ya bayyana sanarwar ta Abbas da cewa wani tawaye kuma ya zarge shi da laifin haddasa gwagwarmayar rike madafun iko tsakanin Falasdinawa. Shi ma ministan harkokin wajen Falasdinawa kuma jigo a kungiyar Hamas Mahmud al-Zahar ya yi watsi da zaben na gaba da wa´adi yana mai cewa:

“Muna ba wa mutane shawara da su guji bin wannan wannan mataki domin idan zasu yi haka ba tare da amincewar al´umar Falasdinu ba ko amincewar gwamnati ba, to ina ganin haka tamkar wata barazana ce ga hadin kan al´umar Falasdinawa.”