Hamas na tunanin neman mafita | Labarai | DW | 09.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas na tunanin neman mafita

Kungiyyar Hamas ta masu kishin Islama, tace zata bukaci tallafi na batutuwa da suka jibanci siyasa da kudi daga kasashen larabawa da kuma wasu kasashen Musulmai.

A cewar daya daga cikin shugabannin kungiyyar, wato Khaled Meshal, sun kudiri aniyar yin hakan ne don yin kandagarki a game da kurarin da kasashen yamma keyi na tsayar da tallafin raya kasa da suke bawa yankin.

A dai jiya ne ministar harkokin wajen Amurka CR tace kasashen yamma zasu tsayar da tallafin da suke bawa yankin, matukar basu amince da kasancewar Israela a matsayin kasa ba.

Kafin dai wannan bayani, na CR, a can baya Ministan harkokin wajen Israela, ya bukaci kasashen duniya dasu kauracewa yankin na Palasdinawa matukar kungiyyar ta Hamas ta kafa gwamnati.