Hamas da Fatah sun yafi juna | Labarai | DW | 20.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hamas da Fatah sun yafi juna

Magabatan Hamas, da na Fatah, sun gana da juna yau juma´a, a wani saban yunƙuri na samar da zaman lahia a ƙasar Palestinu.

An yi wannan tantanawa a zirin Gaza, bisa jagorancin ƙasar Masar.

Ƙungiyoyin 2, sun rattaba hannu, a kan yarjejeniyar yi wa juna afuwa, da kuma haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tabatar da kwanciyar hankali a kasar, da ke fama da tashe tashen hankulla, da matsanancin talauci.

Kakakin ƙungiyar Hamas, Faouzi Barhoum, ya ce an samu mattuƙar fahintar juna, tsakanin tawagogin 2, a cikin wannan ganawa,, irin ta, ta farko, tun bayan da rikici ya yi tsamari a Palestinu.

A nasa gefe, kakakin Fatah, Taoufik Abou Khoussa, ya dangata tantanwa,r a matsayin wata sabuwar madogara, ta ci gaban Palestinu.

Ɓangarorin 2, sun ƙudurci girka komitin haɗin gwiwa, na mussamman, wanda zai zurfafa tunani, a game da hanyoyin magance rikicin gida a wannan ƙasa.

Saidai har ya zuwa yanzu, babu wata cikakar sanarwa, da su ka hiddo, a game da batun girka gwmanatin haɗin kan ƙasa.