1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas da Fatah sun fara tattaunawa

September 25, 2010

Kungiyoyin da ke gaba da juna na Hamas da fatah na kokarin kawar da sabanin da ke tsakaninsu

https://p.dw.com/p/PMQt
Tutar PalisdinuHoto: AP

Kungiyoyin da ke gaba da juna na Hamas da Fatah sun amice da su ci gaba da tattaunawa domin samun daidaituwar baki tsakanin sassan biyu masu gwagwarmayar samar da 'yanci Palasdinu.Yunkurin sasantawar wanda kasar Masar ne ke jagorantarsa, ya zo ne a daidai lokacin da kasar Isra'ila ta fara yin tattaunawar kai tsaye da hukumomin Palasdinu wanda kuma kungiyar Hamas ke yin adawa da shirin.

A cikin wata sanarwa da wakilai kungiyoyin biyu suka fitar a Damaskas sun ce an cimma wata yarjejeniya da za ta kai ga dinke barakar da ke tsakanin kungiyoyin biyu.

Tushen rikicin dai tsakanin kungiyoyin na Hamas mai samun goyon bayan kasashen Siriya da Iran, da kuma Fata wacce kasar Masar ke tallafa wa ya samo asili ne tun a shekara ta 2007 akan iko da yankin Gaza.

Mawallafi:Abdourahamane Hassane

Edita : Halima Balaraba Abbas