1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hama Yakoma gidan kaso

Mouhamadou Awal Balarabe/YBMarch 11, 2016

Gamayyar jam'iyyun adawar Nijar COPA ta bayyana cewar an garzaya da Hama Amadou da ke takarar shugabancin kasa asibiti sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita.

https://p.dw.com/p/1IBwB
Hama Amadou
Hoto: DW/S. Boukari

Dan takarar jam'iyyar adawa a jamhuriyar Nijer Hama Amadou wanda za a fafata da shi a zaben shugaban kasar zagaye na biyu a mako mai zuwa, ya sake komawa gidan kaso bayan ya samu kulawar lafiya kamar yadda wasu magoya bayansa ke bayyanawa.

Wata majiya ta kusa da Hama Amadou ta bayyana cewa dan takarar bai samu kulawar da ta dace ba bayan ciwon idon da ya samu, an dai duba lafiyar idanun nasa ne a wani wuri na daban sabanin birnin Niamey da ake cewa an kai shi dan a duba lafiyar tasa tun da fari.

Wani da bai so a bayyana sunansa ba ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an duba Hama a garin na Filinge ne a gaban likitansa karkashin matakan tsaro, a wannan gari da ya ke zaman kaso tun a watan Nuwamba, inda bayan duba shi a ka sake mai da shi gidan na kaso.

Ousseini Salatou da ke magana da yawun kawancen COPA 2016 ya ce dan takarar ya dade yana fama da ciwon sai dai a jiya ne abin ya yi tsamari.