Hama Amadou da Yawoyi Agboyibo na ziyara Berlin | Labarai | DW | 08.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hama Amadou da Yawoyi Agboyibo na ziyara Berlin

Praministan Jamhuriya Niger, Hama Amadu, da takwaran sa na ƙasar Togo, Yawoyi Agboyibo, sun gabatar da taron mamena labarai, na haɗin gwiwa, a birnin Berlin na nan ƙasar Jamus.

Shugabanin 2, na ci gaba da ziyara aiki, Jamus, a dangane da shirye-shiryen taron ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na G8, da zai gudana a nan Jamus a wata mai kamawa.

Shugabar gwamnatin Jamus, bugu da ƙari shugabar ƙungiyar gamayya turai Angeler Merkel, ta alƙawarta saka batun bada taimako ga ƙasashen Afrika a tsaka-tsakiyar wannan taro.

A hira da yayi da yan jarida, Praministan Niger Hama Amadu, ya ce ƙasahen G8, ba su cika alƙawarin da su ka ɗauka ba, a taron su na shekara da ta gabata a ƙasar Britania.

Idan dai ba manta ba, albarkacin wannan taro, ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na dunia sun alkawarta hafe bashin dalla milion dubu 30, ga ƙasashe matalauta.