1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halittu masu shayarwa

Abba BashirDecember 11, 2006

Wace halitta ce mai shayarwa kuma mara jela, bayan Mutum

https://p.dw.com/p/BvV6
Biri mara Jela
Biri mara JelaHoto: AP

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fitone daga hannun Malama Mairo Usman, Jihar Tawa, Jamhuriyyar Niger. Malamar tambaya take, wai shin, Wace halitta ce mai shayarwa kuma mara jela, bayan Mutum

Amsa : To malama Mairo, dangane da amsar wannan tambaya taki na, na tuntubi Dr. Adamu Abubakar Yarima, Likita a Tarayyar Najeriya, ga kuma abin da ya ke cewa dangane da amsar wannan tambaya taki.

Dr, Yarima: To dafarko dai bari mu fara da sanin amfanin jela ga wadansu Halittu. Ita dai Jela zata iya kasance doguwa ko gajeriya, mai gashi ko mara gashi. Kuma halittun da suke da jela suna amfani da ita ne don abubuwa daban-daban, wadanda suka hada da sadar da sako, daidaituwa, susa , kariya, wasu halittun ma sukan yi amfani da jelarsu domin saboda korar kudaje da kwari da dai sauransu.

Kimiyya ta tabbatar da cewa, Dam-adam ya kasance mai jela a lokacin da yake cikin mahaifar Uwa a matsayin Tayi, kuma tsayin jelar zai kai kusan kashi daya bisa shida na girman tayin, yayin da Mutum yake girma sai jelar ta ringa zukewa, amma duk da haka dai saura yakan ragu, ko da ga manyan Mutane. A wani lokaci akan haifi Jariri da yar-guntuwar jela mai laushi wadda bata da kashi a jikin ta.

Amma dai duk da wannan bayani na kimiyya, Dan-adam an san shi a matsayin Haliita mara Jela, wato maana wadda jelarsa bata fito fili ba. Kuma a tare da Dan-adam a wannan Aji na halittu masu shayarwa kuma marasa Jela, akwai wasu nau’o’I na Birrai kamar su Gorilla, Chimpanzee, Bonobos, da kuma Orangutan. Duk wadannan nau’o’in halittune na Birrai da ba mu da su a Hausa.Haka zalika wasu nau’o’i na halittar Jemage suma basu da jela.