HALINDA YAN GUDUN HIJIRAN KASASHEN EU ZASU KASANCE CIKI. | Siyasa | DW | 10.08.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALINDA YAN GUDUN HIJIRAN KASASHEN EU ZASU KASANCE CIKI.

Majalisun kula da yan gudun hijira sun koka da sabon tsarin EU kan masu neman mafaka na siyasa.

Kungiyar gamayyar turai EU.

Kungiyar gamayyar turai EU.

Wani tsarin da kungiyar EU ta fitar wanda ke daukan matakai na tsananci wajen bada mafaka ta siyasa,ya jawo babbar damuwa a majalisun kula da yan gudun hijira dake kasashe 15 dake kungiyar kafin fadadadta zuwa 25 a watan mayu.

Shugaban majalisar yan gudun hijira na kasar Portugal,Mar=EdaTeresa Tito de Morais,kamar sauran wakilan yan gudun hijiran dake yankin ,tayi imanin cewa wannan sabon mataki da aka dauka yana barazana ga kundun dake kare yan gudun hijira na kungiyar Gamayyar turai,kana ya sabawa dokar kasa da kasa wanda membobin kungiyar suka amince da ita.

Dayake an soke sintiri na kann iyakan kasashen kamar yadda wannan yarjejeniya ya tanada,tace batun kwararan baki masu neman mafaka ya kasance abune da ita Eu zata dauki matakai na tabbatar da kaidojinsa.

A shekarata 1995 ne kungiyar ta Eu ta zartar da yarjejeniyar dage duk wani takunkumi dake haramta tafiye tafiye cikin kasashen da ake kira Schengen,wanda aka rattabawa hannu shekaru 10 da suka gabata a birnin Luxemburg,tsakanin kasashen da suka dauki nauyin gudanarwa watau Jamus,Faransa,Belgium da Netherlands.Yarjejeniyar dai ta hadar da shiga kowace daya daga kasashen idan har mutum na mallakan Visa ko takardar izinin shiga kasa daya daga cikinsu,ba tare da wata matsala ba akan iyakokinsu.

Bugu da kari yarjejeniyar kazalika ta kunshi sauran kasashen Eu da suka hadar da Austria,Denmark,Finland,Girka,Itali,Portugal,Spain ,da Sweden,da wasu kasashe 2 watau Iceland,da Norway,da basa kungiyar ta EU,ayayinda sauran kasashen Eu kamar Britania da Ireland suka ki shiga wannan yarjejeniya.

A dangane da hakane Tito de Morais tace wannan tsattsauran mataki da aka dauka zai kawo matukar damuwa wa yan gudun hujira musamman ma wa wakilan kungiyar ta EU.

A shekarata 1999,akayiwa wannan yarjejeniya gyaran fuska a birnin Tempere dake kasar Finland,inda aka bada kariya ta bai daya wa wakilan kungiyar.A shekarata ta 1992,akasamu takardun neman mafakar siyasa wajen dubu 700,sai dai kungiyar ta koka da yawan wadannan yan neman mafaka.A wancan lokaci Jamus dake tsakiyar Turai ta karbi Bosniyawa yan neman mafaka kimanin dubu 350,ayayinda a shekarata 1995,kasashe 15 dake kungiyar sukayi kira zartar da kudurita yadda zasu rarraba yan gudun hijira dake cigaba da kwarara.

A tsakanin shekarata 1990-1998,an kiyasta cewa a kowace shekara ana samun yan gudun hijira kimanin dubu 857 dake kwarara zuwa turai.A dangane da hakane Directan ke korafin cewa, idan har akayi fatali da yarjejeniyoyi da aka cimma na Schengen da Dublin,babu shakka zai kasance tamkar sabawa dokar kasa da kasace kkannkariya wa masu neman mafaka ta siyasa.Tace bawa kowace kasa ta EU daman daukan kowane mataki kann wannan batu,bazai zame aala wa jamaa ba.

Zainab Mohammed.