1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halinda da ake ciki a Britania

Ministocin harkokin cikin gida daga kasashen kungiyar gamayyar turai ,zasu gudanar da wani muhimmin taro a birnin London ranar laraba da ministan harkokin cikin gida na Britania John Reid,domin nazari kann tsarin yakar taaddanci da kungiyar ke gudanarwa,bisa ga laakari da shirin kai harin taaddanci da aka bankado a makon daya gaba a Britania.Shirin afkawa jiragen dake zirga zirga tsakanin Britaniyan da Amurka dai ya razana kasashen turan,kasancewar zaa iya shigar da ire iren wadannan sinadran cikin jirage,duk da irin matakan tsaro dake da akwai a filayen jiragen saman wadannan kasashe.To sai dai ministan harkokin cikin gida na Britaniya John Reid,yace yanzu babu alamun barazana mai tsanani, kasancewar an cafke dukkan wadanda ake zargi da shirin kai wadannan hare haren,sai dai kawai a dauki tsauraran matakai na yakar taaddanci.

 • Kwanan wata 14.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5y
 • Kwanan wata 14.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5y