1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halinda ake ciki a Iraki yau

Hauwa Abubakar AjejeJanuary 18, 2007

Jerin fashewar bama bamai yau a Iraqi sun halaka mutane kusan 20 a yau alhamis,yayinda a hannu guda firaministan Irakin yace kasar Iraki tana bukatar sojoji kalilan ne kadai na Amurka muddin dai Amurkan zata wadata rundunar sojinta da makamai da kayan aiki.

https://p.dw.com/p/BtwZ
Hoto: AP

Ya zuwa yanzu dai wadanda suka rasa rayukansu sun kai mutum 17 cikin hare haren bam har sau biyar daga safiyar yau kawo yanzu.

Yan sanda sun sanarda cewa bama bamai uku sun fashe a bayan juna a gaban wani kanti a lardin Dora dake kudancin Bagadaza inda yan sunni suke zaune,inda mutane 7 suka rasa rayukansu 20 kuma suka jikkata,a wani bam din kuma ya tashi a tsakiyar birnin inda anan kuma mutane 4 suka halaka wasu 11 suka samu rauni,a wata kasuwa kuma a gabacin birnin na Bagadaza mutane 3 suka rasa rayukansu.

A halinda ake ciki kuma firaministan iraki Nuri al-Maliki yace Iraki zata bukaci sojoji kalilan ne kawai na Amurka muddun dai Amurkan ta wadata dakarun Iraki da makamai da kayan aiki.

Shugaban na Iraki ya kuma amince da cewa sun sunyi kuskure wajen rataye tsohon shugaba Saddam Hussein,amma ya karyata zargin dake cewa kisan ramuwar gayya sukayi masa.

Al Maliki yace idan har sun samu nasarar kaddamar da yarjjeniyar karin makami ga rundunonin kasar,yana ganin cewa nan da watanni 3 zuwa shida masu zuwa bukatarszu ta kasancewar sojin Amurkan a Iraki zata ragu matuka.

A makon daya gabata ne dai shugaban Amurka Bush ya sanarda karin sojoji 21,000 zuwa Irakin,domin tabbatar da zaman lafiya a Bagadaza da lardin Anbar,da wannan karin yawan sojojin Amurka zai kai 150,000 a Iraki.

Batu da ya janyo suka daga membobin majalisar dokokin Amurka,inda wasu kamar senata Hilary Clinton suke ganin karin kudi ga dakarun Amurka shi yafi muhimmanci.

“Tace bana goyon bayan rage kudi da ake baiwa dakarun amurka,amma ina goyon bayan rage kudin ga dakarun Iraki,idan har gwamnatin Iraqin bata cikasa wasu sahrudda ba”.

Maliki cikin wata hira da kafar yada labaru ta Italy yayi suka ga sakatariyar harkokin wajen Amurka Rice bisa kalamam data yi cewa lokaci kawai gwamnatin al-Maliki iraki take jira,yana mai baiwa rice shawara data kau daga yin kalamai da a cewarsa zai iya taimakawa yan taadda.

Firaministan na Iraki ya kuma soki shugaba Bush game da yace gwamnatin Iraki tayi kuskure wajen rataye Saddam,inda ya baiyana kamar ramuwar gayya tayi.

Al-Maliki yace akwai alamun cewa Bush ya fara mika wuya bori yah au game da matsin lamba da yake samu a gida.

Ya kuma yi watsi da zargin dake cewa gwamnatinsa bata daukar tsauraran mataki kan yan shia dake dauke da makamai,yana mai baiyanawa manema labarai cewa yanzu haka ana tsare day an kungiyar sojojin Mahdi 400.

Maliki ya lashi takobin sa kafar wando daya da kungiyoyi dake tada zaune tsaye a Iraki koda kuwa a cewarsa yan sunni shia Qurdawa jamiya ko kuma yan taadda.