Halin tsaro a kara rincabewa a Afghanistan | Labarai | DW | 02.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin tsaro a kara rincabewa a Afghanistan

Tashe tashen hankula da suka addabi yankin kudancin Afghanistan sun yi sanadiyar mutuwar ´yan sanda 9 da ´yan tawayen Taliban akalla 13. Hakazalika wani dan kunar bakin wake ya tada bam cikin mota kusa da wani ayarin motocin dakaru kawance karkashin jagorancin Amirka, inda ya raunata soja daya. Tashe tashen hakulan dai na faruwa yayin da halin tsaro ya rincabe sannan masu ta da kayar baya suka tsananta kai hare hare mafi muni a cikin kasar ta Afghanistan tun bayan hambarad da gwamnatin Taliban kusan shekaru 5 da suka wuce.