1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin tsaro a Chadi

Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince a janye dakarun da ke kare 'yan gudun hijira a Chadi

default

'Yangudun hijira a Chadi

Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da janye dakarunta daga ƙasar Chadi, da jamhuriyar Afirka ta tsakiya. Bai ɗaya wakilan kwamitin sulhu 15 na majalisar suka amince da janye dakarun a ƙarshen shekarar bana. Wakilan kwamtin sun baiwa sakatare janar na majalisar Ban Ki-moon da ya fara janye dakarun daga watan juli mai zuwa, inda za'a kammala janyesu duka a cikin watan disambar bana.  Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta bayana damuwarta bisa shawar. tana mai cewa wannan shawar za ta yi illa ga dubban yan gudun hijira dake zama a yankin.  An dai tura dakaru dubu 3,300 don su maye gurbin dakarun Tarayyar Turai, waɗanda suka janye a bara. Ayyukan dakarun shine kare lafiyar dubban yan gudun hijara da suka fito daga yankin Darfur da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da kuma na kasar ta Chadi da kuma samar da hanyar da za iya kai musu abinci. Da ma dai gwamnatin ƙasar tana neman imma a rage dakarun ko kuma janye su baki ɗaya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal