Halin siyasa a kasar Japan | Labarai | DW | 23.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin siyasa a kasar Japan

Jam´iyar dake jan ragamar mulki a Japan ta zabi Yasuo Fukuda don ya gaji Shinze Abe a matsayin FM a wani mataki na farfado da jam´iyar da kuma kawo karshen dambaruwar siyasa. Fukuda wanda ke goyon bayan karfafa dangantaka tsakanin Japan da makwabtanta na Asiya ana daukarsa a matsayin mutum mai matsakaicin ra´ayi. Ya ka da tsohon ministan harkokin waje Taro Aso don darewa kan kujerar shugabancin jam´iyar ta Liberal Democratic Party. Kimanin makwanni biyu da suka wuce Abe ba zato ba tsammani yayi murabus sakamakon jerin abubuan kunya na siyasa da kuma kayen da ya sha a zaben babbar majalisar dokokin Japan a cikin watan yuli.