1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN RAYUWAR BAKAKEN FATA DAGA KUDANCIN SAHARA A KASAR LIBIYA.

YAHAYA AHMEDApril 9, 2004

Kusan mutane dubu dari 6 zuwa miliyan 1, daga nahiyar Afirka bakar fata ne ke zaune a Libya. Mafi yawansu kuwa sun shiga kasar ne cikin shekarun 1990, a lokacin da shugaba Muammar Gaddafi ke ta kara samun sabani da sauran kasashen Larabawa. Amma a halin yanzu, da kasar Libyan ta sake kulla huldodi da Turai da Amirka, akwai alamun da ke nuna cewa, kyamar da ake nuna wa baki daga nahiyar Afirka bakar fata sai kara habaka take yi.

https://p.dw.com/p/Bvkn
Wani gungun `yan kasar Ghana a wani matsatsen dakin da suke barci a ciki a Tripoli.
Wani gungun `yan kasar Ghana a wani matsatsen dakin da suke barci a ciki a Tripoli.Hoto: AP

Tun shekaru 7 da suka wuce ne wani madinki, wanda ya bukaci kada a ambaci sunansa, ya ce ya zo kasar Libiya daga arewacin Najeriya, bayan tafiyar sati 3 a mota, cikin hamada da suka yi. A halin yanzu dai, yana wani dan shago ne a tsohon garin Tripoli inda yake dinkinsa:-

"A cikin wannan kasar, `yan Afirka bakaken fata na shan wahalhalu daban-daban. Mutan kasar na nuna mana wulakanci. Idan wani ya gama ku da daya daga cikinsu, sai ka ga mutane kusan 10, ko 20 ko ma 30 sun zo sun afka maka da duka. Za su iya ma kashe mutum, ba tare da wani ma ya kula da abin da ya faru ba."

An dai kiyasci cewa, bakake daga yankunan Afirka kudu da Sahara kusan dubu dari 6 zuwa miliyan daya ne ke zaune a Libiyan. Su ne ke sharan ttituna, da wanke motoci, da kwasan shara, da dai sauran duk wasu ayyukan da `yan kasar ba sa son yi.

A zahiri dai, Libiya na daya daga cikin kasashe mafi arziki a nahiyar Afiirka. Amma a can ma, matsaloli kamarsu talauci da rashin aikin yi, sai habaka suke ta yi. A cikin watan Oktoban shekara ta 2000, sai da wata arangama ta barke tsakanin `yan kasar Libiyan da baki daga yankunan Afirka bakar fata.

Kusan bakake 100 ne wasu rahotanni suka ce sun rasa rayukansu. Dalilin wannan arangamar dai, shi ne zargin da `yan kasar ke yi wa wani baki, da suka ce ya yi wa wata `yar kasar fyade. Amma a hukumance an bayyana cewa, wani rikicin da ya barke tasakanin gungun `yan fataucin miyagun kwayoyi masu hamayya da juna, daga Libiyan da bakaken fatar ne, ya janyo wannan tarzomar.

A kofar tsohon garin birnin Tripoli, wadda aka fi sani da suna Bab al-Hurriya, nan ne aka fi samun yawan bakaken fata daga kudancin Sahara, suna kasuwancinsu. Babu abin da ba sa sayarwa.

Amma ko yaya `yan kasar Libiyan ke ganin bakaken fatan? Wani binciken da maneman labaran Jamus suka gudanar a birnin na Tripolis na nuna cewa, ra’ayoyin dai sun bambanta. Wani balaraben Libiyan da aka tambaya, cewa ya yi:-

"Matsala, babu shakka akwai matsaloli da yawa." Da ya ga ana daukar maganarsa ne, sai nan take ya sake ra’ayi ya ce:-

"Ai ba mu da wata matsala game da su. Dukkanmu daidai muke, mu da Afirkawan duk `yan uwan juna ne."

Nan take ne kuma, wani ya tsoma baki daga gefe, ya ce bakaken fatan:-

"Masu fataucin miyagun kwayoyi ne, suna yi wa matanmu fyade, suna kuma yada cutar nan ta AIDS."

`Yan Afirkan dai na cikin wani mawuyacin hali ne a kasar Libiyan. A cikin tsoffin gidajen da suke kusa rushewa suke zaune. A galibi ana ganinsu ne a gungu-gungu. Kuma suna hakan ne don kare kansu daga daukin da a wasu lokutan, matasan kasar ke yi musu.

Game da halin rayuwarsu da matsalolin da suke huskanta dai, wasu bakaken sun bayyana cewa:-

"Mu Afirkawa a nan Libiya, ba a nuna mana adalci. Bakake ne wadanda ba sa samun aikin yi a nan. Akwai da yawa daga cikinmu wadanda ke fama da rashin kudi, da rashin gun zama mai kyau."

"`Yan Libiyan dai ba sa kaunar baki A ko yaushe suna iya kai mana hari. "

"A wasu lokutan da daddare suka afka mana, su yi kaca kaca da dakunanmu, su sace mana `yan kudadenmu su yi tafiyarsu. Libya ba gun kirki ne na zama ba."

Tun da shugaba Gaddafi ya juya hankalinsa zuwa Turai da Amirka ne, a hukumance ma aka zartad da kudurorin da suka shafi zaman `yan Afirka bakar fata a kasar ta Libiya. A cikin watan Maris da ya gabata, majalisar jama’a ta Libiyan ta zartad da wani kuduri, wanda ya takaita tafiye-tafiyen `yan Afirkan a kasar. Duk wadanda ba su da aikin yi ma, kamata ya yi su fice daga kasar. Da yawa daga cikin Afirkawan dai na begen komawa kasashensu. Sai dai babbar matsalar da suke huskanta, ita ce ta rashin kudi.