1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin rayuwa a Zimbabwe

Mansour BBNovember 4, 2003
https://p.dw.com/p/Bvno

Tun ba yau ba jamiyyar adawa ta MDC a kasar zimbabwe ke kiran shugaba mugabe daya sauka daga mafan ikon kasar domin tabbatar da adalci ga yan kasar tare kuma da ceto su daga kangin rayuwa da suke ciki .Wannan batun kuwa ya samo karbuwa a kasashen ketare bisa matsin lam,bar da shugaban ke fuskanta a waje da cikin gida .A wata sabuwea dai ya nunar da cewa jamiyyarsa ta Zanu Pf shugaba mugabe ya fara samun suka daga yayanta bisa tabarbarewar tattalin arzikin kasa da kuma zamantakewa .A yanzu haka dai taron kasa na jamiyyar ta Zanu Pf na karatowa a kasar wanda dole ne a dauki matakin gyara idan har ana bukatar kwalliya ta biya kudin sabulu .Yawancin yayan jamiyyar dai na bukatar ganin an sanya sabbin jini cikin shugabancin jamiyyar a nan gaba kadan .Kamar dai yarda wani da bai so a bayyana sasunansa ba yace a yanzu jjamiyyar ta fada wani tarkon cin hanci da rashawa wanda ke dada dusashe tauraruwar jamiyyar a idanun yan kasar .Wannan dan jamiyyar wanda tsohon kanal ne a soji yace bisa halin rayuwa da yan kasar suka fada a yanzu jamian yan sanda kann nemi abun goro a bayyanar jammaa baya ga irin wannan halayyar ga maaikatan Gwamnatin kasar .A dangane da haka ne shugaba mugabe ya amince da yiwa jamiyyar kwaskwarima domin cimma manufar da aka sanya a gaba .Yawancin wadanda ake masu kallon tamkar bara gurbi ne yan siyasa ne sun hada da wasu na hannun daman shugaba Mugabe da kuma wasu daga cikin ministocinsa a halin yanzu wadanda ke yiwa jamiyyar karantsaye .To sai dai wata majiya tace dole a yi taka tsantsan don kada su koma ga jamiyyar adawa ta mDc wanda hakan tamkar koma baya ne ga jamiyyar ta Zanu Pf .Kamar dai yarda wasu manazartan harkokin siyasar kasar ke cewa a yanzu shugaba Mugabe ya kasance kaden garen bakin tulu a kasar ,bayan da ana da yan kishin kasa a cikin jamniyyar dake mulki a kasar .Suna masu raayin cewa a yanzu babu ruwan sha a kasar ga yunwa da take azzabar yan kasar ga koma baya ta ta fannin tattaklin arzikin kasa .A daura da haka kayan abinci yayi tashin gwauran zabi wanda talakawan kasa sun fada wani irin tarko na ni kyasu .Wani dan kasar mai suna charles Buntau ya dai nuna bukatar dake akwai na shugabas Mugabe ya dauki salo irin na takwaransa na Afrika ta kudu Nelson Mandela domin tabbatar da samun kwanciyar hankali a kasar Shugaba mugabe dai ya kasance a kann karagar mulkin kasar ta zimbabwe shekaru 23 kenan tun bayan da kasar ta sami yancin kanta daga kasar Britaniya .To sai dai tunui suka raba gari da iyayen Gidansa bisa wasu matakai da shugaba Mugabe ke dauka a kasar wanda har yanzu yake cikin batanci daga kasashen ketare .