1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da 'yan jarida da mawallafa ke ciki a sassa dabam-dabam na duniya

October 5, 2004

Har yau ana ci gaba da muzanta wa 'yan jarida da mawallafa a kasashe da dama bisa zarginsu da ta'addanci sakamakon sukan lamirin manufofin gwamnati a rubuce-rubucensu

https://p.dw.com/p/Bvfx

A yau talata ne dandalin bikin baje litattafai na kasa da kasa a birnin Frankfurt zai bude kofofinsa ga maziyarta, wadanda zasu shaida litattafai sama da dubu 350 da masu baje kolin su kimanin dubu 6700 daga kasashe 111 zasu nunar a cikin kwanaki shida masu zuwa. Amma fa a daidai lokacin da ake doki da murnar wannan biki na baje litattafai, akwai mawallafa da ‚yan jarida masu tarin yawa dake fuskantar barazana a kasashensu. Da yawa daga mahukuntan wadannan kasashe ba sa kaunar mawallafa saboda a ganinsu alkalami wani makami ne da ake amfani da shi domin sukan lamirin manufofinsu kuma a sakamakon haka suke bakin kokarinsu wajen murkushesu ko ta halin kaka tare da shafa musu kashin kaza a matsayin ‚yan ta’adda. An ji wannan bayanin ne daga bakin Karin Clark shugabar kwamitin mawallafa na kasa da kasa dake tsare a gudajen kurkuku, reshen Jamus. Al’amura sai dada tabarbarewa suke yi a kasashen Afurka, Asiya da Latin Amurka, saboda matakai da mahukunta da ‚yan tawaye da masu safarar miyagun kwayoyi da sojan sa kai ke dauka domin gisan gilla akan ‚yan jarida da mawallafa. Misali a kasar rasha kadai an kashe ‚yan jarida 125 tun abin da ya kama daga shekara ta 2000. Ko da yake a zamanin baya kwamitin na PEN a takaice ya fi mayar da hankalinsa ne akan mawallafan dake fama da barazana a kasashensu, amma a yanzun ta kan shigar da ‚yan jarida a cikin rahotanninta na rabin shekara sakamakon kashe-kashe na gilla da ake yi musu a daidai lokacin da suke bakin aikinsu. ‚Yan jarida na cikin hali na kaka-nika-yi a kasashe kamarsu China da Maldaviya da Myanmar da Nepal da Vietnam da Iran da ragowarsu. Amma fa matsalar ba ta takaita ba ne akan wadannan kasashen da tun fil-azal aka sansu da muzanta wa 'yan jarida da mawallafa, domin kuwa akwai kasashe da dama dake amfani da abin da aka kira wai matakan murkushe ta’addanci tsakanin kasa da kasa, wanda aka gabatar bayan 11 ga watan satumban shekara ta 2001, domin take ‚yancin fadin albarkacin bakin jama’a, daidai yadda aka tanadar a cikin kudirin kare hakkin dan-Adam na MDD. Misali Amurka ta gabatar da wasu dokokin dake ba da damar tsare mutum har sai illa masha’Allahu bisa dalilin zargin manufofin gwamnati. Mahukuntan Amurka na amfani da sabbin dokokin da aka gabatar domin yin fatali da abin da daftarin tsarin mulkin kasar ya tanada na haramta tsare mutum ba tare da gurfanar da shi gaban shari’a domin amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa ba. A kasashe kamarsu Birtaniya da Denmark da Kanada da kuma Spain, kazalika ana amfani da maganar yaki da ta’addanci domin tace labarai da hana fadin albarkacin baki. Bisa ga ra’ayin Karin Clark za a samu kafar shawo kan wannan mummunan ci gaba ne kawai ta hanyar tsage wa jama’a gaskiyar halin da ake ciki a ko’ina a duniya.