1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin Da 'yan Gudun Hijira Ke Ciki A Sudan

June 28, 2004

Har yau ana ci gaba da fama da matsaloli wajen kai taimako ga 'yan gudun hijirar Sudan daga yankin Darfur

https://p.dw.com/p/Bvie
'Yan gudun hijirar Sudan A Chadi
'Yan gudun hijirar Sudan A ChadiHoto: AP

A lokacin da yake bayani wani jami’in taimakon ‚yan gudun hijira daga kasar Norway, mai suna Tor Valla, yayi nuni da mawuyacin halin da ake ciki yanzun tare kuma da hangen karatowar damina inda al’amura zasu dada rincabewa. Amma babban abin dake hana ruwa gudu shi ne karancin kudi, inda kawo yanzu wani dan kaso ne da bai taka kara ya karya ba ake gabatarwa daga abin da aka kasafta wa kungiyar taimakon ‚yan gudun hijira ta MDD domin gudanar da ayyukanta na taimakon makaurata daga yankin Darfur a yammacin Sudan. An ji irin wanna nbayani daga Helene Caux daga kungiyar ta MDD, inda ta ce ana bukatar abin da ya kai dalar Amurka miliyan 55 domin kyautata makomar ‚yan gudun hijira, amma duka-duka abin da aka samu bai zarce dala miliyan 18 ba. Alkaluma dai na yin nuni da makaurata dubu 200 da aka yi musu sansani a kasar Chadi, amma a hakika ba wanda ya san adadinsu. Akwai bukatar sa ido akan iyaka mai tsawon kilomita 600 kuma da wuya ake iya banbantawa tsakanin ‚yan gudun hijirar da ainifin al’umar kasar Chadi a wuraren da aka kafa musu sansani saboda yawa-yawancinsu ‚yan kabila daya ne. An samu cincirindon daruruwan makaurata a karamin garin Tine dake tsakanin Chadi da Sudan suna jiran motocin kungiyar taimakon ‚yan gudun hijira ta MDD da zasu kwashesu zuwa sansanonin da aka tanadar musu. Wasu sun bi ayarin motocin a yayinda wadansu daga cikinsu kuma suka yi zamansu ba tare da tabbas a game da makomarsu ba, saboda duniya gaba daya an yi fatali da mawuyacin halin da wannan yanki ke ciki. Helene Caux ta ce akan samu gungu-gungu na ‚yan gudun hijirar a wawware ta yadda da wuya a iya janyo hankalin jama’a zuwa ga wannan hali na rashin sanin tabbas a ake ciki. Bisa sabanin yadda al’amura suka kasance a Ruwanda ko Kosovo, a wannan yanki ba ka ganin jerin gwanon dubban daruruwan mutane dake kan hanyarsu ta gudun hijira, sai dai a rika tsintarsu gungu-gungu. A nasa bangaren Tony Raby daga asusun taimakon yara na MDD ya ce ko da yake ba za a iya batu a game da wani bala’i ko wata masifa ba, amma fa muddin aka ci gaba da harde kafafuwa to kuwa, to kuwa nan da ‚yan makonni kalilan masu zuwa, murna zata koma ciki dangane da mummunan bala’in da zai biyo baya. Wannan shi ne ainifin dalilin da ya sanya ake jigilar kayan taimakon abinci ba kakkautawa. Amma taimakon daga kasashen Amurka da na kungiyar tarayyar Turai ko kadan ba zai wadatar ba. Tor Valla daga kasar Norway ya ce a dai wannan marra da ake ciki yanzun kungiyoyin taimakon ba zasu iya warware dukkan matsalolin dake akwai ba, illa kawai su dan sassauta wa ‚yan gudun hijirar radadin da suke fama da shi a rayuwarsu ta yau da kullum. Wannan manufar ce kawai ke ba su kwarin guiwar ci gaba da gudanar da ayyukansu duk kuwa da wahalhalun da suke fuskanta a kullu-yaumin.