Halin da Tsibirin Taiwan ke ciki | Siyasa | DW | 22.03.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Halin da Tsibirin Taiwan ke ciki

Dangantakar Amurka da Sin da Taiwan

default

Zaɓaɓɓen Shugaban Tsibirin Taiwan, Ma Ying-jeou.

Zaɓaɓɓen shugaban Tsibirin Taiwan yayi kira ga Sin data rusa makami mai Linzami da take shirin harbawa tsibirin,kafin ɓangarorin biyu su kaddamar da tattaunawar sulhu.

Nasarar da Ma Ying-jeou na jami'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasa a Taiwan din a jiya dai na mai zama babban alama ne na ingantuwan dangantaka tsakanin tsibirin da Sin,sai dai babu tabbacin hakan inji manazarta.

Ma dai yayi amfani da inganta dangantakarsu da Sin da bayyana damuwa dangane da koma bayan tattalin arzikin tsibirin wajen lashe zaɓen na shugaban ƙasa,inda ya kada Frank Hsieh na jamiiiyyar Demokrat dake mulki.

Professor Liu Bih-rong na jami'ar Soochow,ya bayyana cewar da wannan nasara da jami'iyyar adawar ta samu,za a samu ingantuwan dangantaka tsakanin tsibirin da Sin.Yace hakan na nuni da cewar al'ummomin Taiwan sun mikawa jami'iyyar adawar akalar jagorantar su wajen dangantakar kasuwanci kai tsaye da Sin.

Tsibirin na Taiwan dai ya ɓalle daga ƙasar Sin a 1949 bayan yaƙin basasa,tun daga wancan lokaci zuwa yanzu take cin mulkin gashin kanta,duk dacewar Beijing na mata kallon wani yankin ta ne daya ɓalle,wanda kuma yasa har yanzu take barazanar kai mata mamaye idan har ta sanar da 'yancin kai a hukumance.

Hakan dai ya samu suka daga ƙasashen duniya .Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice tace....

"muna ganin cewar babu yadda zaa samu wani cigaba a irin wannan yanayi na ,duk wani abu da zaa dauki mataki ta ɓangare guda na aiwatar wa ba abune da zaiyi tasiri ba ,kuma duk wani abu dazai haifar da saɓani bashi da kyau musamman ga rayuwar al'umma"

Zaɓaɓɓen shugaba Ma dai yayi alkawarin aiki tare da gwamnatin Beijing ,tare da fatan cimma yarjejeniya dangane da zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu,bayan shekarun saɓani .

Eberhard Sandschneider kwararre kan harkokin siyasar Sin yace gwamnatin Beijing na muradin ganin ta sake mallake wannan tsibiri mai zaman kansa shi yasa take ɗaukar waɗannan matakai nayi mata barazana.

Zaɓen Taiwan din a jiya dai ya dauki hankulan hukumomin na Sin da Amurka,waɗanda baki ɗayansu keda ra'ayi kan tsibirin.

Amurka dai itace ke a gaba wajen sayarwa Taiwan makaman soji ,kuma tana da ikon kare Tsibirin daga kowane hari daga waje.

A jiyan ne kuma al'ummomin kasar suka kada kuri'ar sake sa shiga Majalisar Ɗunkin Duniya,wakilcin da Taiwan ɗin ta rasa tun a shekara ta 1971 wa Sin.Ayayinda ita kuwa Amurka ta sauya dangantakar Diplomasiyya daga Beijing zuwa Tapei a 1979 .