Halin da Sharon yake ciki bayan tiyata
January 5, 2006Faraministan Israela Ariel Sharon a yanzu haka na cikin wani matsanancin hali a wani asibiti dake birnin Kudus, bayan tiyata ta gaggawa da aka yi masa sakamakon bugun jini mai tsananin gaske daya fuskanta, wanda hakan ya haifar masa da tsinkewar jini a kwakwalwar sa.
A yanzu haka dai Sharon mai shekaru 77, na a karkashin kulawa ta musanman, bayan dogon suma da yayi a sakamakon tiyatar da aka yi masa.
Kafin dai fuskantar wannan hali, Mr Sharon ya kasance ne a matsayin mutumin da ake hasashen zai lashe zaben gama gari da aka shirya yi a kasar a ranar 28 ga watan Maris na wannan shekara da muke ciki.
Bayanai dai sun nunar da cewa tuni mataimakin faraministan kasar, wato Ehud Olmert ya karbi ragamar tafiyar da al´amurran gwamnatin kasar kafin Sharon ya samu lafiya.
Ya zuwa yanzu dai Eduh Olmert ya tabbatar da cewa al´amurran mulki a kasar ta Israela naci gaba da gudana , duk kuwa da matsanan cin hali da akasar take ciki a yanzu haka.