1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da matasa ke ciki a gabacin Jamus bayan shekaru 20 na haɗewa

September 30, 2010

Matasa a gabacin Jamus ba su ganin wani banbancin tsakaninsu da takwarorinsu a yammaci ko da yake sun taso ne a wani ɓangare dabam na Jamus kuma akasarinsu na fatan dawowa da zama a yammaci bayan kammala makaranta.

https://p.dw.com/p/PQeb
Ɗaliban sakandaren Karl-Liebknecht-Gymnasium a Frankfurt/OderHoto: Benjamin Hammer

Fankfurt dake bakin kogin Oder yana can ne ƙuriyar gabacin Jamus, aƙalla a bisa taswira. Birnin na nan ne a daidai kan iyaka da ƙasar Poland. Ga da yawa daga Jamusawan yammaci hakan na ma'anar ɗimbim marasa aikin yi da taɓarɓarewar al'amura. Ɗalibai a makarantar sakandare ta Karl-Liebknecht-Gymnasium kan nuna ɓacin ransu game da irin wannan wariya. "A duk lokacin da za a ba da labari game da mu sai kawai batun marasa aikin yi da tsattsauran ra'ayin ƙyamar baƙi ake yi", a cewar Florian Hundertmark dake da shekaru 17 na haifuwa. "Ta haka a matsayin mutum na ɗan yammaci ba zai yi tunanin kirki game da Frankfurt ba."

Florian na tsaye ne tare da Käthe mai shekaru 18 da Jörn dake da shekaru 16 a bakin kogin Oder. Dukkan matasan guda uku ɗalibai ne a sakandaren ta Karl-Liebknecht-Gymnasium. A ɗaya gaɓar kogin na Oder akwai wani ɗan ƙaramin garin ƙasar Poland mai suna Slubice kuma daga can nesa ana iya jin ƙararrawar mujami'ar Marienkirchen tana kaɗawa. "A haƙiƙa ana iya yin abubuwa masu ƙayatarwa a nan saboda wuri ne mai ban sha'awa", in ji Jörn. "Amma mutane sai ƙaura suke yi daga yankin."

Kusan mutane 30.000 suka fice daga Frankfurt

Galibi idan matasa a garin Frankfurt dake bakin kogin Oder na batu game da haɗewar Jamus da yammacin Jamus ba maganar siyasa ko tarihi suke yi ba. Sun fi mayar da hankali ne akan makomarsu a kasuwar ƙodago. Yawan marasa aikin yi a gabacin Jamus da ya kama kashi 11 ɗigo 5 cikin ɗari ya kusan riɓanya na yammacin ƙasar. Kimanin mutane 88.000 ne ke zaune a Frankfurt a shekara ta 1990. Amma a yau shekaru ashirin bayan sauyin da aka samu kusan mutane 30.000 sun yi ƙaura daga birnin. Su ma dai Käthe da Jörn da Florian, bisa ga dukkan alamu, zasu mayar da zamansu ne zuwa yammaci nan gaba. Florian, alal-misali, yana sha'awar nazarin fasahar sarrafa motoci ne a jami'a kuma hakan ba zata yiwu ba sai a yammaci, a cewarsa. "Alhali kuwa inda so samu ne da zan fi ƙaunar zama a nan kurkusa."

Makomar tattalin arziƙi dai ita ce ta banbanta tsakanin matasa na gabaci da yammacin Jamus bayan shekaru 20 da haɗewar ƙasar. In banda wannan akwai dace a tsakaninsu. "Ba rababbiyar al'uma muke ba", in ji Jörn. "Har yau dai akan ji maganar katanga a kawunan mutane, amma a ganina wannan ma sannu a hankali zai gushe." Ɗaliban na sakandare dai sun taso ne a haɗaɗɗiyar ƙasar Jamus saboda an haife su ne tsakanin 1992 da 1994.

Matasa na gabaci da yammacin Jamus sun yi kama da juna

Dangane da al'amuran nishaɗi da al'adu dai kamar kiɗa da wasan motsa jiki da hutu a tsuburin Mallorca na ƙasar Spain ba wani banbanci tsakanin illahirin matasan Jamus. Wannan ma shi ne ra'ayin Thomas Gensicke daga cibiyar bincike ta TNS. Idan dai an kwatanta mutane a gabaci da yammacin Jamus za a ga cewar "matasa su ne ɓangaren da ba wani banbanci tsakaninsu", in ji Gensicke. Shi kansa malamin binciken an haife shi ne a Magdeburg dake gabacin Jamus ya kuma mayar da zamansa zuwa yammacin ƙasar bayan haɗewarta. Ya mayar da ainihin tarihinsa abin gudanar da bincike akai.

Duk da dace dake akwai, amma fa akwai banbanci kamar yadda Gensicke ya nunar. Misali matasa a gabacin Jamus na ɗariɗari da tsarin siyasar ƙasar. "Idan mun tambayi matasa game da ko shin tsarin demoƙraɗiyya na tafiya salin-alin sai su ce abin na buƙatar gyara." Manufa a nan kuwa ita ce siyasar Jamus baki ɗayanta, wadda baƙuwa ce a gabacin ƙasar.

Madalla da haɗewa

Shin wannan ɗariɗari na ma'anar ƙyamar ƙasar ne baki ɗaya? A'a, lamarin ba haka yake ba a cewar ɗaliban makarantar sakantare ta Liebknecht-Gymnasium. "Muna murnar cewa an haɗe", in ji Inka Sörries dake aji na 12. "Jama'a a gabacin Jamus ba ta da cikakkiyar walwala, kamar dai damar tafiye-tafiye a zamanin baya."

"'Yan gabaci", "'Yan yammaci" duk da daidaituwar al'amuran da aka samu akan ji irin wannan banbance-banbance, ko da kuwa taɗi ne tsakanin ɗalibai tare da waɗanda iyayensu suka tashi daga yammacin Jamus zuwa Frankfurt bayan haɗewar ƙasar. A misalin shekaru biyu da suka wuce sun sadu da wasu 'yan samari guda biyu lokacin wani zaman musaya, in ji Käthe. "Na yi mamaki matuƙa ainun kasancewar sun san inda Frakfurt/Oder take."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal