1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da Kiristoci ke ciki a Marokko

Mohammad Nasiru AwalMarch 11, 2007

Ana samun kwararar ´yan mishan daga Amirka a kasar ta Marokko.

https://p.dw.com/p/BvSx
Birnin Marakesh a Marokko
Birnin Marakesh a MarokkoHoto: PA/dpa

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taba Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi al´adu, addinai da zamantakewa a sassa daban daban na duniya.

A kasashen Larabawa, kiristoci na da wani matsayin na musamman. Ko da yake al-Qur´ani ya ba su matsayi na musamman amma ana saka ayar tambaya ko shin haka na ma´anar wani gatanci ne ko kuma wariya? Alal misali a Marokko daya dake cikin jerin kasashen Larabawa masu sassaucin manufofi rayuwar yau da kullum ta Larabawa Kiristoci a wannan kasa na tattatare da matsaloli iri dabam dabam, kamar yadda zaku ji karin bayani a cikin shirin na yau wanda ni MNA zan gabatar.

Madalla. A Marokko Kiristoci na daga cikin tsiraru a wannan kasa, kuma suna fuskantar matsaloli na wariya iri dabam-dabam kamar yadda wani matashi Kirista na kasar ya nunar.

“Idan ina cikin safa sauran fasinjoji wadanda suka sanni ko muke a unguwa guda, kan tambaye ni dalilin da ya sa nake zuwa coci. Mai yasa bana zuwa masallaci yin salla, ai akwai masallatai da yawa a nan. Kuma idan na je neman aiki kuma idan daya daga cikin masu ba da aikin ya sanni kuma ya san ni kirista ne, hakan na nufin ba za su ba ni aiki ba.”

A: Wannan talikin na daga cikin tsirarun kiristoci a Marokko, wadanda yawan bai kai kashi daya cikin 100 na al´umar kasar baki daya ba. Yayin da Turawa kirista ke tafiyar da addinin su a kasar ba tare da tsangwama ba, su kuwa takwarorinsu kiristoci ´yan kasar na fuskantar matsalolin tafiyar da addinin su. Domin a kullum ana zargin su da yin ridda wato suna barin addinin Islama, abin da ya ke haramun a cikin musulunci. Jean-Luc Blac Fasto a majami´ar Evangelika dake birnin Casablanca ya tofa albarkacin bakin sa akan wannan batu yana mai cewa.

“Fatan mu shi ne hukumomin Marokko za´a nuna matsayin su a dangane da wannan batu. Muna bukatar a yi mana bayani dalla dalla. Dokar musulunci wato Shari´a ta haramtawa musulmi canza addinin sa, to amma dokokin kasa da kasa ya amince da canza addinin a cikin Marokko. Saboda haka muke tambaya game da matsayin kasar a dangane da ´yancin dan Adam.”

A: A kullum Fasto Jean-Luc Blanc na shaida yadda musulmi ke amfani da wata doka da ake Dhimmi suna bayyana cewa Islama addini ne na nuna juriya. Wannan dokar da ta samo asali tun a karni na 7 ta tanadi ba da kariya ga Yudawa da Kiristoci. Wannan dokar ta fara aiki tun a lokacin da addinin Islama ke fadada wato lokacin da alal misali Larabawa a arewacin Afirka ke cin kasashen da mafi rinjayen al´umomin Kiristoci ne da Yahudawa, yaki cikin sauri. Ana yarda su ci-gaba da tafiyar da addininsu to amma ba´a amincewa su gina wuraren ibada, kuma dole su sanya tufafi na dabam don a iya bambamta su da sauran mabiya jama´a. Bugu da kari dole ne su biya haraji.

B: Tarihi ya nuna cewa dokar ta Dhimmi ta tanadi tabbatar da musulmi tsiraru akan madafun iko a kasashen da musulmin suka ci su yaki. To sai dai a hakika yanzu abubuwa sun canza. Tun fiye da shekaru dubu da suka wuce kasashen yankin Maghreb suka kasance na musulmi. Saboda haka ga kiristoci kamar masanin ilimin addinai Jean-Luc Blanc yake da muhimmanci a fara wata muhawwara don tantance matsayin dokar ta Dhimmi a wannan zamani. Domin tanadin nuna juriya da dokar ta yi ya sa har yanzu a wasu kasashen Larabawa ba´a yarda Yahudawa da Kiristoci sun ba da shaida a gaban wata kotun shari´ar musulunci.

A: Fasto Jean-Luc Blanc ya yi nuni da cewa duk da dokar ta Dhimmi har yanzu gwamnatin Saudiyya ba ta yarda a gina coci a cikin kasar ta. Saboda haka yake neman a kasa mai sassaucin manufofi kamar Marokko a kara girmama ´yancin Bil Adam da ´yancin gudanar da addini ga kowa da kowa.

“Yana da muhimmanci a gare mu gwamnatin Marokko ta fito karara ta nuna mana yadda zamu tafiyar da huldodin mu da sauran al´umar kasar wadanda ke sha´awar shiga addinin kirista. Ko da yake a halin nan da ake ciki ba ma juya musu baya kai tsaye, amma muna takatsantsan don hana yin wani abu da zai karya dokar kasa.”

A: Yanzu dai Kiristoci baki a Marokko na fatan gwamnati musamman ma gidan sarautar kasar zata kara mai da himma don aiwatar da sauye sauye masu fa´ida wadanda zasu dace da zamantakewar al´umar kasashen Larabawa masu sassaucin ra´ayi. Daya daga cikin masu bawa sarki Mohammad na 6 shawara Bayahude ne, saboda haka fasto Jean-Luc Blanc na ganin wannan a matsayin kyakkyawan misali na juriya da karbar sauran al´umomin hannu bibiyu a Marokko. To amma gammo ka iya juyema kaya. Domin ana nuna fargabar cewa masu kishin Islama ka iya samun karin sabbin magoya baya ganin yadda ´yan mishan daga Amirka ke kara kwarara a kasar ta Marokko. Fasto Blanc na ganin sabuwar farfagandar ta ´yan mishan ka iya zama babbar barazana ga kiritoci na cikin gida.

“Domin ya zamewa manyan majami´u tilas su juyawa masu sha´awar addinin kiristan baya, ya sa yanzu wadannan mutanen na karkata ga kananan dariku na Kirista kamar darikar Mormon wato ´yan majami´ar Latter Day Saint. Ban san ainihin yawan su ba, amma tun bayan 11 ga watan satumban shekara ta 2001 da kuma barkewar yakin Iraki, kungiyoyin ´yan mishan da yawa na Amirka sun shigo Marokko don nasarantar da musulmi.”

A hakika masu kishin addinin Islama a kasar ka iya amfani da wannan halin da aka shiga don farautar dukkan kiristoci a cikin kasar.

“An shiga mawuyacin hali. Wadannan ´yan mishan na kafa kungiyoyin ´yan kirista sannan a wani lokacin ma su na bi gida-gida don yada addinin na kirista. Sun fi samun karbuwa a tsakanin bakin haure wadanda ba su da cikkakun takardun izinin zama cikin kasa. Ya zuwa yanzu hukumomi na jurema wannan yanayin na karuwar kananan majami´u. To amma tambaya a nan ita ce, har zuwa yaushe za´a ci-gaba da haka? Shin musulmi masu rinjaye a kasar zasu ci-gaba da ganin ana yi musu shiga hanci da kudundune?