1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA KASAR AFGHANISTAN TAKE CIKI

Lamurra dai sai kara cakudewa suke yi, a kasar Afganistan, a yayin da ake saran a gudanar da zabe a wannan kasar, a shekara mai zuwa. kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya da yakai wata ziyara a wannan kasar, ya ganewa idonsa, irin halin rashin dadin da kasar take ciki. Hasali ma, dai, jakadan Jamus,Gunter Pleuger,wanda shine ya jagoranci rangadin 'yan kwamitin na majalisar dinkin duniya,zuwa Afghanistan din, a satin daya gabata,ya fada a cikin rahoton sa, cewar, fadace fadace da tashe tashen hankulla dake gudana a wannan kasar, zai iya tarnake duk wani yunkurin gudanar da zabe a wannan kasar. Ya ce, idan dai ana bukatar ganin ayyukan tsaro sun ingantu a wannan kasar, to kuwa tilas ne, a tashi tsaye, a halin da muke ciki.

A cikin ire iren rikice rikicen dake faruwa, a Afghanistan dinne, aka kai kusa ofishin majalisar dinkin duniyar, dake Kandahar wani hari, wanda yayi sanadin jiwa mai gadin wurin rauni tare da wani mutum. A wani harin kuma,sojin kasar Romaniya dake cikin sojojin tsaron lafiya ya rasa ransa,yayin da wani kuma ya samu rauni, a yankin kudu, a cikin wannan kasar.

A yankin kudu din dai, da kudu maso gabas, anata samun afkuwar kai hare hare akan sojojin Amurka dana Afghanistan da kuma jami'an bayar da agaji,hare haren dake ta kara karuwa a kusan kullum. A satin daya gabata ma, wani bam ya tashi a ofishin Oxfom da Save The Chilren, a can Kabul, babbabn birnin kasaer Afghanistan din. A bisa wadannan hare haren ne, ma, yasa majalisar dinkin duniya, da kungiyoyin bayar da agaji, keta rage gudanar da ayyukansu, a bisa kokarin kaucewa kai masu hari. A bisa wani rahoto, a kalla jami'an bayar da agaji 11 ne suka rasa rayukan su, a ciki harda wani dan kungiyar Red Cross, wanda aka halbe,a cikin kai hare haren dake gudana a wannan kasar, tun daga karshen watan Maris zuwa yau. Sojojin Amurka kuma suna tayin arangama da masu yakin sunkuru na kasar, a inda ko ranar Litinin din data gabata,a wannan satin, saida akayi wani dauki ba dadi a wurare daban daban, a cikin kasar,tsakanin bangarorin 2, kamar yadda mai magana da yawun sojojin kanal Rodney Davis ya bayyana.

Akawi dai sojojin taron dangi kimanin 12,500 dake ta faffatawa da 'yan yakin sunkuru na kasar Afghanistan din, tun bayan da Amurka tayi jagorancin ture gwamnatin 'yan Taliban, abun kuma na neman ya faskare su. A halin yanzu dai,wakilan majalisar dinkin duniya da suka kai ziyarar gani da ido, zuwa wannan kasar,sunyi kira ga sakatare janar na majalisar dinkin duniyar, Kofi Anana, da ya dubi lamarin bukatarsu ta, a yi wani taro akan halin da kasar take ciki, ta yadda kasashen duniya,zasu samu damar tattaunawa tare da shiga a cikin lamurran ta yadda za'a iya samun damar warware dunbin matsalolin da suka hada dana tattalin arzikin kasar da siyasa, da kuma uwa uba, batun harkokin tsaro.

 • Kwanan wata 12.11.2003
 • Mawallafi ABUBAKAR D. MANI
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvng
 • Kwanan wata 12.11.2003
 • Mawallafi ABUBAKAR D. MANI
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvng