Halin da bil Adama ke ciki a lardin Darfur na kara yin muni | Labarai | DW | 16.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da bil Adama ke ciki a lardin Darfur na kara yin muni

Hukumar kula da ´yan gudun hijira ta MDD ta nunar da cewa halin da ake ciki a lardin Darfur na yammacin Sudan na kara yin muni a kowace ranar Allah ta´ala. Hukumar ta ce mawuyacin halin da ake ciki yanzu a wannan lardin ya yi daidai da mummunan halin da aka fuskanta a Darfur din a cikin shekara ta 2003. Babban kwamishinan ´yan gudun hijira na MDD Antonio Guterres ya ce yanzu haka mawuyacin halin da ake ciki a lardin ya fara yin tasiri a kasashe makwabta.

Guterres ya ce:

“Yanzu dai Darfur ta zama tamkar wani wuri ne da wata mummunar girgizar kasa ta fi karfi, wanda ka iya yin mummunan tasiri a kan zaman lafiya, tsaro da kuma ´yan Adam baki daya.”