1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI YANZU A ITALIYA BAYAN MUTUWAR SOJOJIN ?ASAR 18, A HARIN DA AKA KAI MUSU A IRAQI.

"Abin takaici. Ni ban san ma ko me zan ce ba kuma, game da abin da ya auku." Italiyawa da yawa ne ke nuna bacin ransu game da harin da aka kai jiya a kan dakarun da gwamnatin kasar ta tura zuwa Iraqi. A harin dai, wanda aka kai jiya a garin Nassiriya, jami'an tsaron Italiya 18 ne suka mutu. A makon da ya gabata ma, an kai hare-hare da dama a kan dakarun mamaye a kasar Iraqin. Amma a wannan lokacin, daukin da ake yi bai shafi Italiyawan ba tukuna. Sabili da haka ne `yan kasar da dama suka yi ta fatar cewa, sojojinsu dai babu abin da zai same su. Kuma za su dawo gida ne lami lafiya. Garin Nassiriyan dai, gu ne da ba a saba tashe-tashen hankulla ba. Hakan ne ma ya sa ministan tasaron Italiya, Antonio Martino, nanata cewa, wannan yankin na cikin wuraren da ake zaman lumana a Iraqi.

A halin da ake ciki yanzu dai, bayan da aka kai wa rundunar Italiyan hari a Nassiriyya, `yan kasar da dama a birnin Rum, sun bayyana matukar bacin ransu ga manufofin da gwamnatin Berlusconi ke bi na tallafa wa Amirka a Iraqi. Mafi yawan jama'a dai na zargin `yan siyasan kasar ne da tsunduma sojojin cikin wani mawuyacin hali da kuma kasada.

Kawo yanzu dai, an tabbatar cewa sojojin Italiya 18 ne suka sheka lahira, sakamakon harin da aka kai musu jiya a Nassiriya. Tun dai yakin duniya na biyu, ba a taba samun asarar yawan sojojin Italiyan a bakin daga, kamar jiya ba. Gaba daya dai, dakaru dubu 3 ne gwamnatin Berlusconi ta tura zuwa Iraqin. Kafin ma a tura sun, sai da jam'iyyun adawan kasar suka nuna kin amincewarsu da shirin. Wannan harin dai, ya sa sun iza wuta a sukar da suke yi wa gwamnatin. Amma shugaban adawa a majalisar dokokin kasar, Francesco Rutelli, ya yi kira ga duk bangarorin siyasan Italiyan da su kauce wa duk wani ka ce na ce kan wannan batu a halin yanzu:.- "Yanzu dai lokaci ne da ya kamata mu sami hadin kan kasa baki daya. Muna nuna zumunci ga `yan rundunar Karabinieri, da kuma iyalann sojojin da suka rasa rayukansu. Muna kurkusa ga duk `yan Italiyan da suka rasa rayukansu a wannan harin, `yan kasa da suka wakilce mu a Iraqin."

Har ila yau dai `yan jam'iyyar gurguzu masu bin akidar neman sauyi, na nan na iza wuta wajen sukar gwamnatin Berlusconi, da kuma anagaza wa Firamiyan da ya dau matakan dawo da sauran sojojin kasar daga Iraqi cikin gaggawa. Shugaban jam'iyyar kwaminis na Italiyan ma, kira ya yi ga murabus din gwamnatin gaba daya.
Duk da wadannan koke-koken dai, Firamiya Silvio Berlusconi, ya dage kan cewar ba zai juya wa Amirka baya ba. Ba zai kuma sake alkibla a kan manufofin da ya sanya a gaba ba. Shi dai Berlusconi, ya dau matakin tura dakarun Italiyan zuwa Iraqi ne, duk da rashin amincewar mafi yawan `yan kasarsa. A lokacin tura dakarun dai, babu wanda ma ya taba zaton cewa, za a sami asarar rayukan wasu daga cikinsu.

Yanzu kuwa da hakan ya auku, babu shakka gwamnatin Italiyan za ta kara kasancewa ne cikin wani mawuyacin hali, inda in ba arziki aka yi ba, al'amura za su tabarbare har ya kai ga kifad da gwamnatin a majalisa.
 • Kwanan wata 13.11.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvnc
 • Kwanan wata 13.11.2003
 • Mawallafi Yahaya Ahmed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvnc