Halin da ake ciki adangane da gobarar bututun mai a Nigeria | Labarai | DW | 27.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki adangane da gobarar bututun mai a Nigeria

Jamian kiwon lafiya na cigaba da fesa magunguna ,domin kashe kwayoyin cuta da zaa iya dauka a inda aka samu gobarar bututn mai ,wanda kawo yanzu ya kashe mutane 260 a hukumance,baya ga wasu da suka jikkata ,ayayinda jamian agaji ke cigaba da binciken wasu mutanen.Hukumar manpetur ta NNPC,wadda bututun tane ya ya barke da gobara a jiya talata a ,yankin arewacin Abule Egba dake jihar Lagos,ta sanar dacewa kawo yanzu adadin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin gobaran yana tsanin 200-250,ijin kakakin NNPC Levi Ajuonuma.Ita kuwa kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross ,ta bakin babban sakaren ta Abiodun Orebiyi,cewa tayi gobarar ta akalla mutane 269 mace,tare da gargadin cewa wasu daga cikin wadanda suke jinya yanzu na iya rasa rayukansu,sakamakon tsananin kuna.Mazauna yankin dai sun shaidar dacewa gobarar da barke ne sakamakon ,satan mai daga bututun da wasu yan ta kife sukayi da sanyin safiyar jiya.