HALIN DA AKE CIKI A YANKIN ASIA:BAYAN TSUNAMI. | Siyasa | DW | 12.01.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A YANKIN ASIA:BAYAN TSUNAMI.

jamian bayar da agajin gaggawa a kasar thailand.

default

Har yanzu dai jamian bayar da agajin gaggawa na kasa da kasa naci gaba da gudanar da aiyukan su a kasashe goma sha biyu da balain girgizar kasa da kuma ambaliyar ruwa ta tsunami ta rutsa dasu.

Ya zuwa yanzu dai kididdiga ta baya bayan nan na nuni da cewa mutane sama da dubu 165 suka rugamu gidan gaskiya sakamakon wan nan balai na igiyar ruwan ta tsunami a waje daya kuma wasu dubbannai suka jikkata.

A misali rahotanni da suka iso mana daga yankin banda Ache na kasar Indonesia inda wan nan igiyar ruwa ta tasunami tafi yin barna mai yawan gaske ta nunar da cewa gwamnatin kasar ta gargadi jamian gudanar da agajin gaggawan dasu zauna a cikin shirin kota kwana na tsammanin murabbukan kawo musu hare hare daga kungiyyar yan tawaye dake cin karen ta babu babbaka a yankin.

Har ilya yau gwamnatin ta Indonesia ta kuma bukaci jamian bayar da agajin gaggawar da kuma dakarun tsaron kasashen ketare dasu zama a cikin shirin ficewa daga kasar a karshen watan maris na wan nan shekara da muke ciki.

Kafafen yada labarun kasar ta Indonesia sun rawaito mataimakin shugaban kasar wato Yusuf Kalla na fadin cewa da zarar wadan nan jamiai su n kammala aikin su kamata yayi su fice daga kasar don gudun kin yin hakan ya jawo wani balain na daban.

Ya zuwa yanzu dai an kiyasta cewa akwai dakarun sojin kasashen Amurka da Australia da Japan da Malaysia da kuma Singapore a yankin na Banda Ache da kuma Sumatra,suna gudanar da aikin bayar da agajin gaggawa.

A waje daya kuma Jim kadan bayan sanarwar wan nan gargadin ne daga mahukuntan kasar ta Indonesia,kungiyyar yan tawayen ta fito fili ta la,anci wan na