Halin da ake ciki a Turkiyya bayan hatsarin jirgin sama | Labarai | DW | 01.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a Turkiyya bayan hatsarin jirgin sama

Jami´an Turkiyya sun sanar da gano baƙaƙen akwatuna biyu, bayan hatsarin jirgin saman ƙasar a jiya Juma´a. Akwatunan a cewar rahotanni abubuwane da za su taimaka, wajen gano musabbabin hatsarin jirgin. Jirgin ƙirar MacDonald Douglas 83 mallakar kamfanin Atlasjet ya yi hatsarin ne, a yankin Isparta dake kudu maso yammacin ƙasar, jim ƙaɗan da tashinsa daga birnin Istanbul. Dukkannin mutanen dake cikin jirgin 57 sun rasa rayukansu. Ya zuwa yanzu dai babu bayanin cewa akwai zagon ƙasa dangane da faruwar wannan hatsari, to amma bincike kan hakan na nan na ci gaba da gudana.