halin da ake ciki a Sri Lanka | Siyasa | DW | 20.05.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

halin da ake ciki a Sri Lanka

Bayan shekaru 27 na yaƙi dakarun gwamnatin Sri Lanka sun murƙushe ´yan tawayen Tamil Tigers.Wane hali ake ciki yanzu a yankin ?

default

Halin da ake ciki a yankin Sri Lanka da yayi fama da yaƙin basasa

Wata ƙididdiga da Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, tace kimanin mutane dubu tamanin zuwa dubu ɗari ne suka rasa rayukansu a tsawon shekaru 27 da aka shafe ana yaƙi, tsakanin ´yan tawayen ƙungiyar Tamil Tigers da sojojin gwamnatin Sri Lanka.

Lamarin da ya sanya Majalisar Ɗinkin Duniya yin kira da babban murya ga gwamnatin Sri Lanka data ƙyale jami'an bada agaji shiga yankin na Tamil, domin bada agaji tare kuma da ganewa idanunsu halin da duban ´yan gudun hijiran yaƙin ke ciki.

Yanzu haka dai babban magatakar Majalisar Ɗinkin Duniya Ban ki-Moon ya shirya kai wata ziyara gaggawa zuwa arewa maso gabashin ƙasar Sri Lanka a ranar Juma'ar nan, domin ganewa idanun sa halin da ´yan gudun hijira kimanin dubu 80 da yaƙin ya rutsa da su ke ciki a halin yanzu.

A jawabin daya gabatar jin kadan bayan da gwamnatin Sri Lanka ta bada sanarwar kawo karshen yakin basasan na shekaru 27 da yan kungiyar ta Tamil ,Ban ki-moon ya jaddada kiraye kirayen da Majalisar Ɗinkin Duniya ta sha yiwa gwamnatin Sri Lanka, data bari wakilan Majalisar kai agajin gaggawa ga fararen hula, tare kuma da zama teburin sulhu da yan ƙabilar ta Tamil domin sake gina yankin.

Ban ki-Moon yace :zanci gaba da baiyana damuwata, ga halin tsaro da kuma halin ƙunci da fararen hula ke ciki.kuma dalilin da ya sa kenan na shirya zuwa ƙasar ta Sri Lanka, domin ziyarar sansanonin ´yan gudun hijira. Zan kuma gabatarwa gwamnatin Sri Lanka bukatar Majalisar Ɗinkin Duniya na bada agaji tare da sake tsugunar da fararen hulan da wannan bala'i ya rutsa da su.

Sauran ƙasashen duniya da suka bi sahun Majalisar Ɗinkin Duniyar, wajen kira ga gwamnatin Sri Lanka data sassauta takunkumin data sanya a yankin na ´yan Tamil, sun haɗa da Ƙungiyar Tarayyar Turai da Amirka,inda wani jami'n ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Amirka yayi kira ga gwamnatin Sri Lankan data gaggauta ɗaukan matakan sasantawa da ´yan ƙabilar ta Tamil

A jawabin daya gabatar ga lokacin al'umar ƙasar shugaban Sri Lanka, Mahinda Rajpakse yayi alkawarin ɗaukar matakan kare haƙin ´yan ƙabilar ta Tamil, tare da sake gina yankunan nasu da yaki yayiwa ɓarna.Amma ata bakin shugaban wata Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama na ´yan Tamil da ake kira People Union for Civil Liberties,Dr V Suresh yace wannan jawabi na shugaban na Sri Lanka zance ne kawai,domin kuwa alkawura ne da suka saba ji,ba tare da sun gani a kasa ba.Yace :wayannan kalamai tamkar iho ne bayan hari,ina so mu duba tarihin wannan gwamnati game da abin da ya shafi yankin tamil,babu wani ƙamshin gaskiya game da alkawuran daya ɗauka,wannan ba shine karon farko da yake ɗaukan wayannan alkawura ba.Mu duba gabashin ƙasar mana,tun shekaru biyu da suka gabata akayi alkawarin ɗaukan matakan inganta yankin,amma har yanzu shiru kake ji.kuma kowa yasan wannan yankin na yan Tamil ne.wannan ba karamin cin amanar jama'a da kuma yaudara bane, abin da kuma kesa mutane yanke ƙauna akan tafarkin mulkin demokiraɗiyyan ƙasar.

Yanzu haka dai bayan da gwamnatin kasar ta nuna wata gawa da tace na shugaban yan tawayen na tamil ne ,da aka kashe a lokacin da yake kokarin tserewa,jam'ar kasar naci gaba da gudanar da bukukuwa,bayan hutun da gwamnati ta bayar a jiya laraba.

Sai dai yan kabilar ta Tamil dake gudun hijirah a kasashen duniya daban daban da yawan su yakai miliyan daya da rabi tare da sauran kungiyoyin kare hakkin bil'adama da Majalisar Ɗinkin Duniya suna kira daga kafa wata hukuma ta musanman da zata binciki zargin cin zarafi, tare da karya yancin bil'adama da akewa ɓangarorin biyu,a wannan yaƙi daya hallaka mutane kusan dubu 100.

Mawallafi: Baban Gida Jibril.

Edita: Yahouza Sadissou Madobi