1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a Somalia

Yahouza S.MadobiJuly 24, 2006

Magoya bayan kotunan musulunci sun shirya zanga zangar ƙin jinnin Ethiopia

https://p.dw.com/p/Btyu
Hoto: AP

Shugabanin kotunan musuluncin a Somalia, sun zargi gwamnatin riƙwan,ƙwarya da kitsa wata maƙarƙashiya, tare da haɗin gwiwar, ɗaya daga madugun rundunonin sa kai, da su ka yaka yi saranda a watan da ya gabata.

A yamacin jiya ne, Mohamed Afrah Qanyare, ya sauka a binrin Baidoa fadar gwamnatin riƙwan ƙwarya.

Kakakin gwamati, da ya bada wannan sanarwa, bai bayana dalilan ziyara ba.

A wani labarin kuma, a ƙalla mutane dubu 3 ne, masu goyan bayan kotunan Islama, su ka shirya zanga zangar nuna ƙin jinnin dakarun Ethiopia a ƙasar Somalia.

Masu zanga zangar sun ƙona tutar Ethiolia a filin ƙwalan Mogadiscio, tare da bayana kalamomin Allah tsine ga hukumomin ƙasar.

Kazalika, magoyan bayan kotunan Islama, sun bayyana shirie shireynda su ke na na buɗe yaƙin jihadi ga Ethiopia.

A yayin da ya ɗau magana, a wannan gagaramin taro, shugaban hukumar zartaswa, ta dakarun kotunan islama Sheick Sharif Sheik Ahmed,ya ce mayaƙan sa, a shire su ke, su fafata da rundunar Ethiopia.

Ranar juma´a da ta wuce,shugaban kotunan Musuluncin Cheick Ɗahir Aweys, yayi kira ga yan Somalia, zuwa Jihadi, domin yaƙar Ethiopia, da ta hito hili, ta bada goyan baya ga gwamnatin riƙwan ƙwarya.

Rahotani daga Baidowa, cibiyar gwamnatin, sun ambata cewar Ethiopia ta tura dakarun ta, a birnin domin kariya ga gwamnatin da ke fuskantar barazanar dakarun kotunan islama.