Halin da ake ciki a rikicin Israila da Hizbullah | Labarai | DW | 09.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a rikicin Israila da Hizbullah

A ƙalla mutane goma sha uku suka riga mu gidan gaskiya wasu ashirin kuma suka jikata a farmaki ta jiragen sama da Israila ta kai a ƙauyen Ghaziyeh a kudancin Lebanon. Harin ya auku ne a yayin da jamaár yankin ke janaízar wasu waɗanda suka rasu a hare haren baya da Israilan ta yi. Israilan ta kuma kai hari a wani sansani na yan gudun hijirar Palasdinawa a Lebanon inda mutum ɗaya ya rasa ran sa wasu da dama kuma suka sami raunuka. Israilan ta ce ta kai harin ne da nufin afkawa gidan wani ɗan takifen Hizbullah. Tun da farko sojin Israilan sun rarraba ƙasidu a birnin Tyre a ƙasar Lebanon dake gargaɗin jamaá su kasance a cikin gidajen su domin kaucewa zafafan hare hare da suke shirin aiwatarwa. A waje ɗaya kuma a ƙalla sojin Iraila uku ne suka sheƙa lahira a yayin musayar wuta da dakarun Hizbullah a kudancin Lebanon, yayin da Hizbullahin ta kuma jikta wasu sojojin biyu a arewacin Israila.