1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a lardin Aceh na Indonesiya

January 14, 2005

Ko da yake ayyukan taimako na tafiya salin-alin a lardin Aceh na Indonesiya, amma a bangaren siyasa ana fama da rashin sanin tabbas ta la'akari da yakin basasar da ya ki ci ya ki cinyewa a wannan lardi

https://p.dw.com/p/Bvde

Makonni uku bayan mummunar masifar nan ta girgizar kasar da ta haddasa mahaukaciyar igiyar ruwan da ta rutsa da yankuna da dama na kudancin Asiya, a can lardin Aceh mai fama da yakin basasa, an sake komawa ga rikicin siyasar dake addabar lardin na kasar Indonesiya. Jami’an taimako na kasa da kasar dake gudanar da ayyukansu a wannan yanki tilas ne su yi rajista a gun sojoji kuma ba su da ikon fita daga biranen Banda Aceh da Meulaboh sai tare da rakiyar soja. Shi kansa mataimakin shugaban kasar Indonesiya Yussuf Kallah ya fito fili ya bayyana cewar wajibi ne dukkan dakarun soja na kasashen ketare dake ba da gudummawa a matakan taimakon su bar kasar Indonesiya nan da watanni uku masu zuwa. Dalilin da ya bayar shi ne wai jami’an taimakon na fuskantar barazana daga dakarun kungiyar tawaye ta GAM mai neman ballewar Aceh daga Indonesiya. Amma ita kanta kungiyar ta fito fili ta musunta wannan zargi. An saurara daga bakin kakakinta Zaini Abdallah yana mai cewar:

Kai tsaye bayan afkuwar masifar tsunami ne kungiyar GAM ta gabatar da tayin tsagaita wuta, kuma har yau kungiyar na kan wannan tayi nata.

Ba zato ba tsammani dai, ministan harkokin wajen Indonesiya Virayuda da ya kai ziyara Berlin ya sa kafa yayi fatali da tayin da kasashen gamayyar Paris Club dake ba da lamuni suka yi wa Indonesiya na saurara mata biyan basussukan dake kanta har tsawon watanni 12 masu zuwa. Amma daga baya, a cikin wata hira da tashar Deutsche Welle tayi da shi, yayi gyara ga wannan matsayi da ya dauka, inda yake cewar:

Ba fatali muka yi da wannan tayi ba, abin da muke bukatar sani shi ne akan wani sharadi ne za a saurara mana biyan basussukan. Kawo yanzun dai Indonesiya ba ta sako-sako da wadannan basussuka kuma tana so ta ci gaba akan haka, saboda fargabar da take yi cewar wannan mataki na daga wa’adin biyan basussukan har tsawon shekara daya ka iya zama mummunar illa a gare ta.

Ko da yake wannan maganar ta shafi cancantar kasar ta Indonesiya dangane da karbar rance ne, amma ga alamu masu gwagwarmayar rike madafun ikon kasar kokari suke su fake da guzuma domin su harbi karsana. Domin kuwa ana iya samun kazamar riba daga daruruwan miliyoyin na dalar Amurka da ake gabatarwa don taimako, kuma sojan Indonesiya ne zasu fi cin gajiyar lamarin, wannan shi ne ainifin dalilin da ya sanya Indonesiya ke dari-dari da maganar sarara mata wa’adin biyan basussukan. A cikin ‚yan makonni kalilan masu zuwa dai gaskiya zata bayyana a kuma fahimci ko wane ne ke da ta cewa a Jakarta, fadar mulkin kasar ta Indonesiya.