HALIN DA AKE CIKI A KUDANCIN ASIA:BAYAN GIRGIZAR KASA DA AMBALIYAR RUWA. | Siyasa | DW | 31.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A KUDANCIN ASIA:BAYAN GIRGIZAR KASA DA AMBALIYAR RUWA.

wasu daga cikin mutanen da suka tsira a can kasar bangladash

default

Ya zuwa yanzu dai yawan mutanen da suka rasa rayukan su a kudancin Asia da gabashin nahiyar Africa sakamakon girgizar kasa da kuma ambaliyar ruwa,a yanzu haka ya haura sama da mutane dubu 135.

A kuwa ta bakin ministar harkokin kasar Sweden Laila Freivalds, cewa tayi da alama yawan wadan da suka rasun a yanzu haka ya fara dosar dubu dari biyu.

Minista Laila dai ta fadi hakan ne jim kadan bayan dawowar ta daga kasashen Yankin na Asia a matsayin wata ziyarta ta gani da ido.

Bugu da kari Mr Laila ta kara da cewa kafin tasowar ta izuwa gida taga jiragen ruwa na isowa da gawarwaki na mutane fal a cikin su akai akai ,wanda hakan yake tabbatar da wan nan hasashe da tayi

Rahotanni dai a yanzu haka sun shaidar da cewa mafi yawa daga cikin wan nan jumla ta sama da muka fara ambata na yawan mutanen da suka rasa rayukan nasu sun fi fitowa ne daga kasar Indonesia.

Bugu da kari Rahotannin sun kuma tabbatar da cewa wadan da suka jikkata sakamakon wan nan al,amari nan naci gaba da karuwa ninkin ba ninkin na akan adadin wadan da suka rasa rayukan nasu.

Ya zuwa yanzu dai jamian bayar da agajin gaggawa na kasa da kasa na can naci gaba da gudanar da aiyukan su a wadan nan kasashe da wan nan balai ya rutsa dasu.

Babban dai abin da wadan nan jamian sukafi mayar da hankalin su kai shine na samar da kyakkyawan ruwan sha da abinci da kuma magunguna ga wadanda suka jikkatan.

A waje daya kuma bisa wan nan abu daya faru ga wadan nan kasashe a yanzu haka ya haifar da tsayawar komai cik game da shirye shiryen gudanar da bukukuwan shigowar sabuwar shekara da kasashe daban daban na duniya suka saba yi a dai dai wan nan lokaci.

Daukar wan nan mataki kuwa daga ire iren wadan nan kasashe ya biyo bayan wani mataki ne na nuna alhini da kuma tausayi ga iyalan wadan da wan nan balai ya rutsa dasu a wadan nan kasashe na kudancin yankin na Asia da kuma Gabashin nahiyar Africa.

A waje daya kuma kasar Italiya ta bukaci daggauta shirya taron kolin kasashe masu karfin masana,antu na duniya da akafi sani da suna G8 a turance don duba yiwuwar kara tallafawa kasashen da wan nan balai ya afkawa.

Yin wan nan taro a cewar mahukuntan na Italiya ya zama wajibi bisa la,akari da irin halin da dubbannin mutane ke ciki a wadan nan kasashe goma sha daya da ambaliyar ruwa ta tsunami ta rutsa dasu.

A waje daya kuma kasar Biritaniya tace wan nan taro da kasar italiya ke kiran da a gudanar, ba a shirye shiba tun fil azal a don haka bata ga wani alfanu na gudanar dashi ba.

To amma duk da haka a can baya mahukuntan na Birtaniya sun kara yawan kudin tallafin da suka bawa wadan nan kasashe da a yanzu adadin su ya kai dalar Amurka miliyan hamsin.

A yayin da ake cikin wan nan musayau miyau kuwa a waje daya kwamishinan dake lura da bada tallafi na kungiyyar Eu Louis Micheal yace shirye shirye na nan akan hanya na shirya taron kokon bara na kasa da kasa don tallafawa kasashen da wan nan balai na girgizar da ambaliyar ruwa ya afkawa.

A cewar Kwamishinan za a gudanar da wan nan taron ne a ranar sha daya ga watan janairun sabuwar shekara a can birnin Geneva.

A daya barin kuma kasar Indonesia tace a shirye take ta dauki nauyin shirya taron kolin kokon bara don a tallafawa kasashen da balain girgizar kasa da ambaliyar ruwa ta shafa.

A cewar ministan harkokin wajen kasar ,wato Hassan Wirajuda, wan nan taro zai gayyaci kasashe 23 na duniya da kuma kasashe 10 na kungiyyar kudu maso gabashin nahiyar ta Asia a hannu daya kuma da kungiyoyi na kasa da kasa.

Ibrahim Sani.