Halin da ake ciki a kasar Iraqi | Labarai | DW | 08.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a kasar Iraqi

Rahotanni daga Iraqi na cewa a kalla sojin Amurka hudu sun rasa rayukan su a wani dauki ba dadi a garin Qusayba dake kan iyaka da Syria. Tsawon kwanaki sojin Amurka dana Iraqi suke ta fafatawa da yan tawaye a yankin domin fatattakar su kafin zaben da zaá gudanar a kasar Iraqin a ranar 15 ga watan Disamba . Hukumomin sojin Amurkan sun ce sun kashe a kalla yan tawaye 34 tun bayan da aka fara dauki ba dadin . A wata arngamar kuma wasu yan bindiga dadi sun bude wuta akan wata mota a birnin Bagadaza inda suka kashe mutane goma sha uku.