1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A KASAR IRAKI

Wadanda su ganewa idanunsu sun bayyana cewa wasu mutane dake wucewa cikin mota kirar BMw mai budaddiyar kai ne sukayi wannan harbin wa sojojin na Amurka a wannan gidan shan mai.Nan take sauran sojojin Amurkan dake nan sukayiwa wadannada aka harban zobe,inda bayan nan ne aka tafi dasu asibiti.Duk dacewa daruruwan mutane sun ganewa idanunsu wannan hadari,babu wata sanarwa daga kakakin sojin Amurka kann wannan batu.
A yan makonni biyu da suka gabata ana yawaita samun jerin gwanon motoci a gidajen mai dake kasar ta Iraki,abunda ke nuni da karancin mai a wannan kasa dake da arzikin man petur.Dakarun na Amurka dai sun danganta karancin mai da hare hare da ake cigaba da kaiwa bututuwan mai,boyewa da masu ababan hawa keyi,ga kuma matsalar karuwan yawan motoci dake zorga zirga wajen dubu 250 tunda Amurka ta sanar da mamaye a aranar 1 ga watan mayu.
To sai dai a hannu guda kuma ana cigaba da kira da karin kaiwa dakarun na Amurka hari,dama yan kasar ta iraki dake aiki dasu.Wannan kira kuwa na kunshe ne cikin wasu takardu da wata kungiya dake kiran kanta Free Mujahedeen ke yayatawa a harabar jamiar Mosul.
Ayayinda a mahaifar Sadam Hussein dake Tikrit,Commandan rundunar Amurka ya danganta yawan hare hare da ake kai musu da magoya bayan tsohon shugaba Sadam Hussein.Lieutenant Colonel Steve Russel,yace gano wadannan tsageru zai kasance abu mawuyaci domin sun da dangantaka na kut da kut da Sadam.yace binciken wadannan mutane ba karami aiki bane,wadanda ka iya kasancewa da tsohon shugaban Irakin wanda kuma baa san inda yake ba tun ficewarsa daga birnin Bagadaza.
Dakarun na Amurka dai sun maida hankali wajen neman Sadam da magoya bayansa a garin na Tikrit,mayakan suinkuru da Amurkawan ke zargi da kashe musu yanuwa sama da 190,tun bayan Amurka ta sanar da mamayen wannan kasa. Amurkawan dai na zargin magoya bayan Sadam da daukan nauyin biyan yan kasar ta Iraki domin kaiwa sojojin su hari,wanda ya dada rikitar da dabarunsu na gano wadanda kann kai musu ire iren wadannan hari.
A dangane da irin barazanar wannan harin ne yanzu jakadan kasar Bangladash ya fike daga Bagadaza da sauran jamiansa.Sanarwara gwamnatin kasar na nuni dacewa Jakadar Sarwar Hossain yanzu haka na tafi da harkokin kasar ne daga Jordan,saboda barazanar harin Rokoki a Bagadaza.Bangladash,kasa ta uku a jerin kasashen musulmi ta nuna adawa da harin da Amurka ta jagoranta akan Iraki,kana tace bazata tura dakarunta akarkashin tutar Mdd domin tabbatar da tsaro a wannan kasa ba.
 • Kwanan wata 08.12.2003
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnE
 • Kwanan wata 08.12.2003
 • Mawallafi ZAINAB AM ABUBAKAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvnE