1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a kasar Iraki.

May 11, 2004

Ana cigaba da dauki ba dadi tsakanin magoya bayan muqtad al-sadr da Dakarun Amurka a kewayen Najaf da Kufa.

https://p.dw.com/p/Bvjk
Dakarun Amurka a kusa da Najaf.
Dakarun Amurka a kusa da Najaf.Hoto: AP

Magoya bayan sanannen limamin yan shia na Iraki,Muqtad al Sadr,sun lashi takobin kai hare hare wa dakarun Amurka da kawayenta a sassa daban daban na Iraki,a wani sako ta kassete na Video da suka gabatar a yau talata.Wannan Kasset wadda suka aike da ita sashin labaru na kafar yada labaran Associate Press,na bayyana hotunan wasu mutane 10 dake sanye da bakaken tufafi maza da mata,dauke da makamai da suka hadar harda da gurneti,ayayinda muryar mace da namiji daga cikinsu ke gabatar da sako cikin harshen larabci.,wanda ke dada jaddada cewa zasu sadaukar da rayukansu domin ganin bayan Amurka da kawayenta a wannan kasa.sakon na kara jaddada cewa Iraki zai zama tamkar wani Vietnam ne,idan har aka taba lafiyar Al Sadr.Bugu da kari vedeon ya kuma bayyana yadda sojojin sukayi ta harba Gurneti a cikin dare.Kana muryar namiji nacewa,mayakansu sun kai hari wa ayarin sojin Amurka.

Wannan sakon ya fito ne yini guda bayan dakarun Amurkan sun sanar da kashe 35 daga cikin mayakan limamin yan shiyyan da ake kira al-madhi,a fadan fito na fito daya dauki yini biyu yana gudana tsakanin bangarorin biyu a birnin Bagadaza.

Rundunar Amurkan dai ta lashi takobin ganin bayan mayakan na al Madhi,tare kuma ta cafke limamin su da a halin yanzu ke cigaba da kasancewa a garin Najaf mai tsarki.A yau ne dai mazauna garin yan shiyyan dake Sadr a kusa da Bagadaza,suka fara tayar da ginin Headquatan al-Sadr wanda tankunan da jiragen yakin Amurka suka rusa,a harin da suka kaiwa ginin.

To sai dai sabon gwamnan jihar Najaf da Amurka ta nada, ya bayyana cewa ya fadawa dakarun taron dangindasu sassauta hukuncin kisan gillan da sukewa al Sadr,a wani mataki na kokarin kawo karshen dauki ba dadin dake cigaba da gudana tsakanin bangarorin biyu.gwamna Adnan al-Zurufi,wanda aka nada a makon daya gabata,ya bayyana cewa gwamnatin Iraki a karkashin jagorancin Amurka ,ta amince da jinkirta batun gurfanar da limamin yan shiyyan,har sai bayan yan Irakin sun karbi mulkin kai a ranar 30 ga watan gobe idan mai duka ya kaimu lafiya.

Al Sadr dai ya shige garin na Najaf ne a farkon watan Afrilun daya gabata,bayan hukumomin Amurka sun sanar da bada izinin cafke shi dangane da zargin da ake masa na hannu cikin kisan gilla da akawa,abokin adawarsa kuma limamin yan shiyyan masu sassaucin raayi a watan Afrilun shekara data gabata a gari na najaf.

Tun daga wannan lokaci ne ake fafatawa tsakanin magoya bayansa da sojojin Amurka da Britania,da sauran Sojin taron dangin a kudancin birnin Bagadaza.A wani dauki ba dadi daya gudana a daren jiya,yan Iraki 5 suka rigamu gidan gaskiya,ayayinda wasu 14 suka samu raunuka,a garin Kufa,kamar yadda majiyar Asibitin yankin yayi nuni dashi.To sai dai wakilin jammiyar yan shiyyan dake Najaf ya shaidawa manema labaru cewa ,ayau an sake farfado da yunkurin sasantawa tsakanin mayakan Amurkan dana Limamin yan Shiyan.

To sai dai a hannu guda kuma wata kungiyar fafutukan kare hakkin Biaadama ta yi kira ga magabatan Amurka da Britania,dasu dakatar da musantawa tare da azabtar da Sojojinsu kewa yan Iraki dake tsare a gidajen yarin Irakin.Bayyana hotunan Prisononi tsirara da irin azaba da sojin ke gallaza musu na cigaba da samun suka daga bangarori daban daban na duniya,batu da yanzu haka ya jawo bincike daga bangaren hukumomin kasashen biyu.

Ayayinda a yau ne kuma Rasha tayi kira ga sauran yan kasar dake Iraki dasu gaggauta ficewa daga wannan kasa,bayan kisan gillan da akawa wani Dan kasar tare dayin garkuwa da wasu biyu,wata guda bayan irin wannan yanayi da kasashen duniya suka koka dashi.Jamian Diplomasiyyahn Rashan,sunce yan kasar uku na aikin samar da wutan lantarki a wannan kasa da yaki ya lalata lokacin da aka cafke su.Jiya da rana ne dai wata mota dauke da mayaka da makam,ai sukayi motan dake dauke da yan Rashan kofar rago,akan hanyarsu ta komawa Bagadaza .bayan kammala aiki,wannan shine karo na biyu da Rashan ta fuskanci wannan matsala a Iraki,batu daya jawo Suka daga alummar kasar.Halin ake ciki kenan a Iraki,kuma babu wanda yasan ranar da zaa dasa aya,tare kuma da samun kwanciyar hankali a wannan kasa.

Zainab AM Abubakar.