HALIN DA AKE CIKI A KASAR HAITI. | Siyasa | DW | 02.03.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A KASAR HAITI.

A TUN BAYAN FICEWAR SHUGABA JEAN ARISTIDE DAGA KASAR HAITI A MATSAYIN DAN GUDUN HIJIRA;KASAR A YANZU HAKA TA FARA KOMAWA TURBAR ZAMAN LAFIYA.

MUTANE NA MURNAR ZAMAN LAFIYA A BABBAN BIRNIN KASAR HAITI.

MUTANE NA MURNAR ZAMAN LAFIYA A BABBAN BIRNIN KASAR HAITI.

A yayin da yan tawayen kasar Haiti suka samu nasara game da tursasawa Shugaba Jean Aristide Murabus, daga karagar mulkin kasar tare da Ficewa a matsayin dan gudun hijira,a yanzu haka yan tawayen sun mayar da hankalin su kann yin sintiri don tabbatar da doka da oda a babban birnin Kasar wato,Port Au Prince.

Duk kuwa da wan nan sintiri da yan tawayen keyi a hannu daya kuma akwai dakarun sojin kiyaye zaman lafiya na kasashen Amurka da Faransa da kuma wasu kasashe na yankin Karibeyan da tuni suke iso kasar don gudanar da aikin tsaro tare da kwantar da tarzomar daka iya tasowa.

A yanzu haka dai akwai dakarun sojin kiyaye zaman lafiya na Amurka a kalla guda dari biyu dake cikin kasar ta Haiti,kuma a nan gaba ana sa ran zuwan wasu da yawan su ya ninka wadanda suka fara isa a baya yawa.

A daya wajen kuwa kasar Faransa a yanzu haka nada dakarun sojin kiyaye zaman lafiyar a kalla guda 140 dake cikin kasar ta Haiti.

Duka dai kwamandojin rundunar sojin kasashen biyu sun shaidar da cewa ba a basu umarnin tarwatsa rundunar yan tawayen dake cikin babban birnin kasar ba,domin a cewar su an aiko su kasar ne kawai su tsare mutanen kasar da kuma kayayyakin gwamnati.

Bisa kuwa rahotanni da suka iso mana daga kasar da dama daga cikin masu saye da sayarwa na kasar tuni sun koma bakin harkokin cinikin su a kann titunan babban birnin kasar,to sai dai kuma suna fuskantar yan matsaloli nan da can sakamakon cibiyoyin bincike da yan tawayen suka kafa a gurare daban daban na babban birnin.

A wata sabuwa kuma da dama daga cikin mutanen babban birnin kasar na maraba da ficewar shugaba Aristide daga kasar domin a cewar su wata alama ce ta samun sauki na kakani kayi da suke ciki,wanda suke zargin Jean Aristide da jefa su a ciki,to amma kuma tuni shugaban ya karya wan nan zargi.

A yanzu haka dai babban abin da yafi daukar hankalin yan tawayen a kasar ta Haiti shine,wace dama za,a basu ta taka rawa a cikin sabuwar gwamnatin da za,a kafa a nan gaba.

A waje daya kuma sakataren harkokin waje na Amurka Colin Powell yace batun shigo da yan tawayen cikin gwamnatin wucin gadi a kasar ta Haiti bai ma taso ba,domin a cewar sa da da dama daga cikin su nada kashin kaji a tsuliyar su kuma hakan ba zai dace ace sune suke wakilcin al,umma ba.

A dangane da haka Powell yace zasu ci gaba da kokari wajen ganin sun tabbatar da cewa babu wani dan tawaye daya shiga cikin gwamnatin da za,a kafa a nan gaba.

A dai tun jiya litinin babban Jojin kasar Boniface Alexandre,wanda aka nada a matsayin shugaban kasar ta Haiti na wucin gadi ya bace daga idanun jama,a san nan kuma ya sakawa bakin sa sakata na rashin cewa komai dangane da halin da ake ciki a kasar.

Shi kuwa shugaba mai gudun hijira Jean Betrand Aristide yana can yanzu haka a kasar Africa ta tsakiya a matsayin dan gudun hijira,amma duk da irin wan nan yanayi da yake ciki bai daina ci gaba da sukar lamirin kasar Amurka ba.Wanda bisa hakan jamian gwamnatin kasar suka fara kosawa dashi tare da duba batun ingiza keyarsa izuwa kasa ta gaba da itace a baya aka shirya zai zauna a matsayin dan gudun hijirar.

Wan nan dai rikici na siyasar kasar ta Hati ya samo asali ne a tun bayan da Jamiyyars shugaba Jean Aristide ta lashe dukkanin zabubbukan yan majalisun kasar a shekara ta 2000 data gabata. Wanda a shekarar 1991 sojojin kasar sukayi masa juyin mulki amma kasar Amurka ta dawo dashi kann mukamin sa da karfin tuwo.

Daga tun wancan lokaci kuwa ya zuwa lokacin daya fice daga kasar ya fuskanci shirye shiryen makarkashiyar neman daukar ransa har kashi uku daga bangaren yan tawayen amma kuma abu yaci tura.