HALIN DA AKE CIKI A KASAR HAITI. | Siyasa | DW | 09.03.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A KASAR HAITI.

DAKARUN KIYAYE ZAMAN LAFIYA NE A NAN KE KE YIN BARAZANA GA WASU TSAGERU MAGOYA BAYAN TSOHON SHUGABAN KASAR:

default

A yayin da wakilai guda bakwai a kasar Haiti ke shirye shiryen zabar sabon Faraminista a kasar, kwanaki daya bayan an rantsar da Boniface Alexandre a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya,a yau talata sai gashi tsageru magoya bayan tsohon shugaban kasar na zanga zangar boren lallai a dawo da Jean Betrand Aristide izuwa gida don ci gaba da rike mukamin sa na shugaba.

Tsagerun magoya bayan na Aristide rahotanni sun shaidar da cewa sun tare hanyar shiga babban birnin da manya manyan duwatsu don jiran jiran wanda za,a bayyana a matsayin sabon Faraministan kasar.

Bugu da kari Rahotannin sun kuma nunar da cewa tsagerun sun dauki wan nan matakin ne a matsayin shirin kota kwana da hargitsa lamarin tsaro a kasar,kamar yadda suka yi ikirari a baya muddin dai ba,a dawo da tsohon shugaban a matsayin sa na daba ba.

A hannu daya kuma,wadan nan wakilai na mutane bakwai rahotanni sun nunar da cewa tuni sukayi shakulatin bangaro da ire iren furucen tsohon shugaban na nuna cewa har yanzu shine cikakken shugaban kasar Haiti,ta hanyar ci gaba da musayar miyau na zabar sabon faraministan kasar.

A dai yau talata ne a wani lokaci wakilai guda bakwai zasu bayyana sunan mutumin da suka zaba a matsayin sabon faraministan kasar ta Haiti.

Bayanai dai daga kasar a halin yanzu sun nunar da cewa,dakarun sojin kiyaye zaman lafiya na kasashen ketare dake kasar tare da hadin gwiwar jamian tsaron kasar naci gaba da sintiri a babban birnin kasar da kuma kewayen sa don tabbatar da doka da kuma oda.

A waje daya kuma tsohon shugaban kasar Jean Betrand Aristide ya fito fili yace jamian kasar Amurka ne suka tursasashi ficewa daga kasar izuwa kasar africa ta tsakiya a matsayin dan gudun hijira,a don haka har yanzu shine cikakke kuma zababben shugaban kasar ta Haiti.

Jean Betrand Aristide yaci gaba da cewa yana nan yana adddu,ar Allah ya dawowa da kasar sa zaman lafiya mai dorewa,a hannu daya kuma da jan kunnen magoya bayan sa dasu rungumi matakai na samun wanzuwar zaman lafiya a fadin kasar baki daya.

A cewar wani madinki dan kasar ta Haiti mai suna Bertrand Exilus,abin da kasar Amurka tayiwa Jean Aristide bai dace ba kuma hakan ba demokradiyya bane,domin a cewar sa Aristide zabar sa akayi amma kuma Alexandre shugaban kasar na yanzu ba zabar sa akayi ba.

Shi kuwa sabon shugaban Boniface Alexdandre cewa yayi a yanzu haka gwamnatin sa na kokarin yadda za a shirya gudanar da zabe ne a kasar,to ammma kafin nan yanzu kasar na fuskantar matsaloli na rashin abin ci da dangogin su.

A don haka Alexandre yayi kira da kasashe masu hannu da shuni dasu kawo musu dauki don ganin komai ya tafi dai dai ba tare da fuskantar wani cikas ba.

A wata sabuwa kuma kakakin fadar white House Ricahard Boucher ya karyata zargin da tsohon shugaban kasar ta Haiti ya yiwa Amurka da cewa tursasashi akayi ficewa daga kasar.

Richard Boucher yaci gaba da cewa babu ko ja Jean Aristide murabus yayi da kansa ya kuma fice daga kasar a matsayin dan gudun hijira izuwa kasar Africa ta tsakiya.