HALIN DA AKE CIKI A KASAR AFGANISTAN. | Siyasa | DW | 03.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A KASAR AFGANISTAN.

HOTON DAN AFGANISTAN NE KE DAUKE DA KAYAN ABINCI DAGA CIKIN WANDA KUNGIYYAR RED CROSS KE RABAWA A KASAR.

default

Babbar kungiyyar bayar da agajin gaggawa a kasar Afganistan da akafi sani da suna Medecins Sans Frontiers ta bayar da sanarwar daina gudanar da aikin da takeyi a kasar ta Afganistan har zuwa wani dan lokaci a nan gaba.

Daukar wan nan mataki da wan nan kungiya tayi bisa bayanan da suka iso mana nada nasaba ne da wani kwanton bauna da akayiwa mutanen ta biyar akan hanyaar su ta zuwa birnin Kabul daga yankin Badghis dake da nisan kilomita 550 daga birnin na Kabul,wanda hakan yayi ajalin su ba tare da bata lokaci ba.

Daga cikin mutane biyar din uku daga kasashen ketare suka fito sauran biyun kuma yan cikin kasar ta Afganistan ne

A cewar kakakin wan nan kungiyya ta Medecins Sans frontiers,Vicky Hawkins dukkanin wasu aiyukan bayar da agaji da kungiyyar mu take gudanarwa a fadin kasar ta Afganistan mun tsayar dashi har zuwa wani lokaci. Amma babban abin da zamufi mayar da hankali a kai yanzu shine nazartar halin rashin tsaro da yadda zamu shawo kann al,amarin kafin ci gaba da gudanar da aikin mu yadda ya kamata.

Wan nan al,amari dai a cewar rahotanni da suka iso mana shine mafi muni a tun lokacin da aka fatattaki gwamnatin masu tsattsauran raayi ta yan taliban a shekara ta 2001 data gabata.

A waje daya kuma masu nazarin siyasar kasar na ganin cewa daukar wan nan mataki da kungiyyar ta MSF tayi ba karamar illa zai haifarwa kasar ba ,musanmamma bisa laakari da irin yawan maikatan da take dasu a cikin kasar ta Afganistan.

Masu nazarin sunci gaba da cewa akwai alamun yan fadan sari ka noken da kuma na kwanton bauna ka iya yin amfani da wan nan damar wajen ci gaba da cin karen su babu babbaka wajen ingiza wutar rikice rikice da kuma daukar rayukan bayan Allah.

A daya hannun kuma masu sharhin siyasar na ganin cewa wan nan mataki da kungiyyar ta MSF ta dauka ka iya zama kafa da ragowar kana nan kungiyoyi dake aikin bayar da agajin gaggawa a kasar ka iya dauka.

Wan nan dai kungiyya ta kasance fitatciya wajen gudanar da aikin bayar da agaji a duniya bamki daya,musanmamma a kasar ta Afganistan wanda hakan ne ma yasa aka bata kyautar Nobel na tabbatar da zaman lafiya a shekara ta 1999.

Kafin dai shugaba Hamid Kharzai ya tashi izuwa Amurka a yau Alhamis sai da yayi Allah wadai game da wan nan hari da aka kaiwa wadan nan mutane biyar.

Shugaba kharzai ya kuma shaidar da cewa game da matakan tabbatar da tsaro a kasar a yanzu hajka a iya cewa Allah son Barka,to amma babban abu dake damun yan kasar shine kangi na Talauci da kuma fatara,wanda a ganin sa na daya daga cikin abubuwan dake haifar da ire iren wadan nan munanan aiyuka.

Ita kuwa mdd kira tayi da kasashe da suka ci gaba na duniya dasu kara taimakawa da dakarun kiyaye zaman lafiya izuwa kasar ta Afganistan don kyautata matakan tsaro a fadin kasar baki daya.

Ibrahim Sani