Halin da ake ciki a Italiya a game da zaben da aka gudanar | Labarai | DW | 11.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin da ake ciki a Italiya a game da zaben da aka gudanar

Jamiyyar masu sassaucin ra´ayi a Italiya, da tsohon shugaban kungiyyar Eu kewa jagoranci, wato Romano Prodi tace itace ta lashe zaben gama gari da aka gudanar a kasar.

To amma ya zuwa yanzu, tuni yan jam´iyyar jari hujja da Faraminista Silvio Berlusconi kewa jagoranci a kasar tayi watsi da wannan furuci.

Ya zuwa yanzu dai sakamakon zaben na majalisar wakilai na nuni ne da cewa jam´iyyar ta masu sassaucin ra´ayin nada kashi 49 da digo 8 ne cikin dari, ita kuwa jamiyyar ta Shugaba Berlusconi nada kashi 49 da digo 9 ne cikin dari.

Bugu da kari daga majalisar dattijai kuma rahotanni na nuni ne da cewa da alama jam´iyyar masu sassaucin ra´ayi ce keda alamun lashe zaben da yawan kujera daya akan jamiyyar ta Faraminista Berlusconi.

Kafafen yada labaru dai sun rawaito cewa da alama cikakken sakamakon zaben zai kasance ne da kunnen doki a tsakanin jam´iyyun biyu.