HALIN DA AKE CIKI A IRAQi. | Siyasa | DW | 09.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQi.

WASU MABIYA DARIKAR SUNNI KE NAN RIKE DA BINDIGOGI DON JIRAN TSAMMANNIN KOTA KWANA.

default

A yayin da wasu yan kasar iraqi ke bikin tunawar da kifar da gwamnatin Saddan Hussain a matsayin shekara daya cif,a dai dai lokacin ne kuma yan darikar shia da sunni keci gaba da fafatawa da dakarun sojin hadin gwiwa a wasu yankuna na kasar ta iraqi.

Haka kuma magoya bayan darikun biyu sun kuma yi kurarin aikawa da mutanen kasar Japan da suke tsare dasu izuwa lahira. A hannu daya kuma tare da ragowar mutanen da suke tsare dasu yan wasu kasashe na ketare.

Rahotanni dai da suka iso mana sun nunar da cewa mabiya darikun biyu sun dauki wan nan matakin ne bisa hujjar tursasawa dakarun hadin gwiwar janyewa daga cikin kasar ta iraqi dungurun gum.

A waje daya kuma mahukuntan kasar ta Japan sunci alwashin ci gaba da ajiye sojin nasu a kasar ta Iraqi duk kuzwa da kurarin da mabiya darikun biyu sukayi na aikawada wasu sojin kasar ta Japan da suke tsare dasu izuwa lahira.

A yanzu haka dai bayanai daga kasar ta iraqi sun tabbatar da cewa dakarun sojin hadin gwiwar sun tsagaita da bude wuta kann gungun mabiya darikun biyu,a can garin falluja don bayar da damar gudanar da taron cimma dai daito a tsakanin shugabannin dakarun hadin gwiwar dana shugabannin darikun kasar da kuma mambobin gwamnatin rikon kwarya na iraqin don tattauna hanyar shawo kann wan nan al,amari.

To amma a daya hannun dan jaridar dake daukarwa kamfanin dillancin labaru na AFP hoto ,ya raiwato cewa yayin da yake gudanar da aikin sa akan hanyar sa ta zuwa garin falluja,yau juma,a yaga ana dauki ba dadi a tsakanin dakarun hadin gwiwar da magoya bayan darikar sunni a garin Abu gharib,wanda keda nisan kilomita 10 daga birnin Bagadaza.

Shi kuwa Paul Bremer shugaban rikon kwarya na iraqi cewa yayi daukar wan nan mataki na tsagaitawa da bude wutar,zai bayar da dama ga mutanen dake yankunan da ake fafatawa karbar taimakon agaji da akan basu a hannu daya kuma da yin janaizar wadan da suka ruga mu gidan gaskiya a lokacin gudanar da wan nan arangama data wanzu na tsawon kwanaki shida.

A cewar gidan talabijin din Aljaeeza mutane sama da dari uku ne suka rugamu gidan gaskiya a lokacin wan nan dauki ba dadin na kusan mako daya,banda kuma wasu sama da dari biyar da suka jikkata.

A daya hannun kuma bayanai sun tabbatar da cewa dakarun sojin hadin gwiwar 40 sukace ga garin ku nan a lokacin wan nan fafatawa ta kwanaki shida.

Bugu da kari rahotanni daga garin kut sun shaidar da cewa dakarun sojin Amurka sun maye gurbin dakarun sojin kasar Ukrain da bataliyar sojin su dake kasar ta janye su sakamakon dauki ba dadin daya dinga wakana a tsakanin su da mabiya darikar shia.

A wata sabuwa kuma,wani babban jamiin soji na kasar Russia yace bisa dukkannin alamu mahukuntan Amurka basu da niyyar janye sojin su daga kasar ta iraqi kamar yadda magoya bayan wadan nan dariku ke nema,kin yin hakan a cewar jamiin ka iya kara rura wutar rikice rikicen kasar ta iraqi wanda idan baayi hankali ba ka iya zamowa yakin basasa da zai farraka kasar ta iraqi izuwa gida uku,wato yan darikar shia da sunni da kuma kurdawa.

Bisa wan nan hasashe jamiin yaci gaba da cewa dole ne mdd ta fito fili ta taka rawar daya dace wajen tabbatar da gwamnatin dimokradiyya a kasar ta iraQI,domin yin hakan a cewaer sa shine kadai zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiya a fadin kasar baki daya.

IBRAHIM SANI.