HALIN DA AKE CIKI A IRAQI. | Siyasa | DW | 30.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

HOTON WANI MUTUMIN FALLUJA NE DA IYALANSA KAN HANYAR SA TA YIN KAURA IZUWA NEMAN MAFAKA.

default

A yanzu haka dai rahotanni daga kasar ta iraqi sun shaidar da cewa a yau juma,a dakarun sojin Amurka sun fara janyewa daga garin na Falluja.

Bugu da kari rahotannin sun nunar da cewa a dai dai lokacin da sojojin suka fara janyewa a dai dai lokacin ne kuma wasu jamian sojin na Amurka suka fara wata tattauwar cimma sulhu a tsakanin su da wakilan mutanen garin na Falluja.

Babban makasudin wan nan tattaunawa a cewar bayanai da suka iso mana itace ta a samar da wanzuwar zaman lafiya mai dorewa mai kuma ma,ana a fadin garin baki daya a hannu daya kuma da wasu yankuna na kasar ta iraqi.

Bayanai dai sun nunar da cewa da zarar sojojin na Amurka sun kammala ficewa daga garin na Falluja,za a kafa wata tawagar jamian tsaro na cikin gida su a kalla guda dubu daya da dari daya wanda wani tsohon janar karkashin mulkin Saddam Hussain zaiwa jagoranci.

Daukar wan nan mataki da sojojin na Amurka sukayi masu sharhin abin da kaje yazo sun nunar da cewa abune daka iya taimakawa wajen samo bakin zaren warware irin tashe tashen hankula da ake fuskanta a fadin kasar ta iraqi baki daya.

Kafin dai cimma daukar wan nan mataki daga bangaren sojin na Amurka koda a jiya sai da rahotanni suka nunar da cewa sojojin na Amurka sunyi amfani da kananan jiragen yaki wajen kaiwa garin na Falluja hare hare bisa manufar murkushe aiyukan tsagerun dake kai musu hare hare da suka kiyasta da cewa sun kai a kalla guda dubu biyu.

A wata sabuwa kuma a Lokacin sallar Juma,a a garin Kufa Mutumin da sojin na amurka suke nema ruwa a jallo wato Moqtadar Sadr ya fadawa magoya bayan sa cewa babu gudu babu jada baya wajen ci gaba da nuna adwar su ta tsana da kyama da sukewa dakarun sojin hadin gwiwar da suka mamaye musu kasa.

Moqtadar Sadr yaci gaba da cewa babu ko ja kasar Amurka kasa ce dake yaki da Addinin musulunci da kuma musulmai a don haka ya rage ga musulman su hada karfi da karfe guri guda wajen yakin makiyan nasu.

Shugaban mabiya darikar ta Shaiawa yaci gaba da bayani da kakkausan harshe cewa matukar yana da rai ba zai janye irin maganganun daya fada akan kasar ta Amurka a baya ba sai dai ma abin da ya karu.

A waje daya kuma har ya zuwa yau juma a dakarun sojin na Amurka naci gaba da yiwa garin na Najaf kawanya a matsayin jiran tsammanin murabbuka na afkawa garin da yaki.

A daya hannun kuma tattaunawa a tsakanin shugabannin kabilun yankin da jamian yan sanda na garin naci gaba da gudana na nemo bakin zaren sasanta rikicin tare da rarrashin dakarun na Amurka da kaga su kai harin soji cikin garin na Najaf.

Domin yin hakan a cewar bangarorin biyu ka iya kara tada yamutsi a cikin garin kamar yadda hakan ke gudana a garin Falluja da kuma wasu yankuna na kasar ta iraqi.

A yayin da ake cikin wan nan hali na kiki kaka wasu yan fadan sunkuru sun kaiwa cibiyar dakarun sojin kasar Spain hari to amma rahotanni sun nunar da cewa babu wani soja daya daya ji rauni ko kuma ya rasa ransa.

Bayanai dai sun nunar da cewa kasar ta Spain tuni ta janye dakarun ta guda 1,300 daga kasar ta iraqi ragowar da kawai sukayi saura sune guda dubu daya dake gudanar da aiyukan tattara ragowar kayayyakin da kasar take dasu a kasar ta iraqi.

Suma kuma ragowar a cewar rahotanni da suka iso mana za a kammala kwashe su yan makonni kadan masu zuwa.

IBRAHIM SANI.