HALIN DA AKE CIKI A IRAQI. | Siyasa | DW | 29.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

HOTUN BABBAN JOJIN IRAQI DA FARAMINISTA IYAD ALAWI DA KUMA PAUL BREMER LOKACIN MIKA MULKI DA KUMA KARBA A BIRNIN BAGADAZA.

default

Rahotanni daga iraqi sun nunar da cewa kwanaki daya da mika mulki hannun yan kasar iraqi da dakarun sojin Mamaye sukayi bisa jagorancin Amurka har yanzu tsugune tashi bata kare ba game da rashin wanzuwar zaman lafiya a wan nan kasa.

Rahotanni daga kasar sun shaidar da mutuwar a kalla mutane biyar a gurare daban daban na wan nan kasa sakamakon tashin wasu bama bamai.

A misali a cewar bayanan da suka iso mana mutane ukun wanda dukkannin su sojojin Amurka ne sun rasa rayukan nasu ne sakamakon wani bom daya tashi a kann hanyar da suka bi da motar dake dauke dasu a cikin birnin bagadaza.

Ragowar biyun kuma fararen hula ne tsageru yan kasar ta iraqi wanda su kuma sun bakunci lahira ne bayan sun kai wani hari ga izuwa ofishin yan sanda dake arewacin Birnin na Bagadaza.

A hannu daya kuma wata majiya mai karfi daga dakarun sojin hadin gwiwar ta tabbatar da cewa wasu yan fadan sari ka noke sun kaiwa wani babban jamiin yan sanda a Karbala hari da wasu kana nan makamai to amma m ajiyar bata tantance irin yawan mutanen da suka rasa rayukan su ba ko kuma suka jikkata.

A wata sabuwa kuma kwanaki daya bayan karbar mulki faraministan kasar ta Iraqi Iyad Alawi ya tabbatar da cewa dakarun sojin hadin giwa zasu mika musu tsohon shugaban kasar ta iraqi wato saddam Hussain a gobe laraba idan allah ya kaimu kuma a ranar alhamis a fara tuhumar sa a gaban wata kotun kasar bisa irin laifuffukan daya kwaba a lokacin mulkin sa na danniya da kuma take hakkokin yan kasar.

Faraminista Iyad Alawi yayi alkawarin tabbatar da adalci da kuma gaskiya a lokacin sauraron tuhumar tsohon shugaban kasar ta iraqi da zai gurfana a gaban kuliya a cewar sa a ranar alhamis ta wan nan makon da muke ciki.

A dai can baya shugaban da zai jagoranci sauraron wan nan sharia ta Saddam hussain wato Salem Chalabi ya tabbatar da cewa Saddam Hussain da wasu na hannun daman sa goma sha daya zasu zamo a karkashin ikon gwamnatin rikon kwarya ta iraqi to amma wajen tabbatar da tsaro na fili dakarun sojin hadin gwiwa ne zasu ci gaba da lura da wan nan bangare.

Wadan nan dai kalamai na shugabannin biyu shine ya kawo karshen tantamar da akeyi na yadda makomar tsohon shugaban na iraqi zata kasance a bayan mika mulki hannun yan kasar.

Bugu da kari Iyad Alawi yayi alkawarin cewa wan nan zaman kotu ba zai dauki wani lokaci mai tsawo ba kamar yadda ake zato game da yankewa Saddam da Mukarraban sa hukunci,to amma hukunci irin wan nan yana bukatar sai anyi karatun mun natsu a cikin sa.

Shugaban yaci gaba da cewa dole ne ayi hakuri game da wan nan tuhuma ta Saddam Hussain dana hannun daman nasa domin akwai batutuwa da daman gaske da za a duba a lokacin wan nan tuhuma kama dai daga bacewar mutane sama da miliyan daya a hannu daya kuma da takewa wasu dubbanni yan kasa hakkin su a lokacin mulkin tsohon shugaban na iraqi.

Tabbatar da adalci a lokacin wan nan shiria shine zai tabbatarwa da duniya cewa da gaske muke wajen tabbatar da zaman lafiya da lumana bisa tafarkin mulkin dimokradiyya a fadin kasar baki daya a cewar Iyad Alawi.

A waje daya kuma wata jarida ta kasar masar mai suna Al Akhbar buga wani labari tayi a shafin ta na farko a yau talata dake nuni da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba a iraqi duk kuwa da mika wan nan mulki da dakarun sojin hadin gwiwa sukayi.

Bugu da kari jaridar taci gaba da cewa ita kuwa gwamnatin rikon kwarya ta kasar dole ne tayi aiki tukuru wajen jan hankulan yan kasar nasu mara mata baya don cimma burin da aka sa a gaba.

Ibrahim Sani