HALIN DA AKE CIKI A IRAQI. | Siyasa | DW | 06.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

SOJOJIN AMURKA A IRAQI LOKACIN SINTIRIN INGANTA HARKOKIN TSARO.

default

Ya zuwa yanzu dai faraministan iraqi Iyad Alawi yace gwamnatin sace ta bawa dakarun Amurka bayanin inda yan fadan sari ka noke yan kungiyyar abu musab Al Zarqawi bayanin inda suke boye wanda hakan nema yasa dakarun Amurkan suka kai wani mummunan hari a jiya litinin a maboyar tsagerun dake garin falluja.

Wan nan hari yayi sular mutuwar mutane a kalla guda goma ban da kuma wasu da daman gaske da suka jikkata.Haka kuma a dai wan nan lokaci dakarun sojin Amurka guda uku ne suka ce ga garin ku nan.

A cikin wata sanarwa da ofishin Alzarqawi ya fitar yau talata ya sanarwar ta tabbatar da cewa tuni gwamnati ta daura damarar yaki da yan taddas da kuma aikin taaddanci dake faruwa a kai a kai a wasu yankuna dake fadin kasar ta iraqi.

A wata sabuwa kuma wani dan uwa ga tsohon shugaban kasar iraqi Ezeddin Al majid ya karyata wani labari da jaridar New york Times ta buga na cewa shine yake daukar dawainiyar kula da wadanda suke kaiwa sojojin Amurka hare haren kwanton bauna dana sari ka noke a yankuna daban daban na kasar ta iraqi.

Wan nan babban jamii ya karya wan nan zargi da cewa bashi da tushe balle kuma makama.

Rahotanni a daya hannun kuma sun shaidar da cewa wutar rikice rikice dake faruwa a kasar ta iraqi na karuwa ne sakamakon katsalandan da wasu yan kasashen ketare keyi ne musanmamma daga kasashen Jordan da kuma Syria.

A waje daya kuma wasu mutane yan bindiga dadi dake kasar ta iraqi sunci alwashin kisan Abu musab Al zarqawi matukar bai fice musu daga cikin kasar ba.

Wan nan kungiya ta yan bindiga dadin da suka sawa suna Salvation Movement tace wan nan rana ta talata itace rana ta karshe da suka bawa Al zarqawin tare da mutanen dake boye shi ko kuma suke rufa masa baya nasu fice daga kasar ko kuma dukkannin su su bakunci lahira babu shiri.

Wan nan kungiyya a cewar wata sanarwa da yayaanta suka bayar kuma gidan talabijin na Aljaeera ya yada ta tabbatar da cewa ta dauki wan nan matakin ne bisa irin kiyan kiyashi da Abu musab Al zarqawi ya janyowa daruruwan yan iraqi fararen hula da basu ji basu gani ba.

A don haka yan kubngiyyar ta Salvation Movement sun shaidar da cewa tuni suka daura damarar ci gaba da laluben Al zarqawin don ganin an samu wanzuwar zaman lafiya a fadin kasar ta iraqi baki daya.

Bugu da kari wan nan kungiya ta kuma bukaci masu bawa Al zarqawi goyon baya dasu daina yin hakasn domin kuwa ba masoyi bane ga yan kasar ta iraqi bisa la,akari da irin balain daya janyo na asarar rayukan yan kasar bila a dadin.

Ya zuwa yanzu dai kasar Amurka ta kara yawan kudin data ce zata bawa duk mutumin daya yi sanadiyyar kashe Abu musab Alzarqawin izuwa dalar Amurka miliyan 25.

A wata sabuwa kuma faraministan Biritaniya Tony Blair a karo na farko ya tabbatar da cewa da wuya ne a samu makaman nan na nukiliya da ake zargin kasar iraqi da mallaka a halin yanzu.

Idan dai za a iya tunawa a shekara ta 2002 kafin kaddamar da yakin iraqi Tony Blair ya taba fadin cewa babu ko ja kasar ta iraqi nada makaman nukiliya dana goba wanda hakan ne ma ya haifar Amurka da mukarraban ta suka farwa kasar ta yaki.

Ibrahim sani.