1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

.: HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

MINISTAN HARKOKIN WAJEN IRAQI HOSHIYYAR ZEBARI.

default

Kamar kullum dai a yauma bata canja zani ba game da tashe tashen bama bamai a can kasar iraqi. A bisa rahotannin da suka iso mana Birnin Bagadaza ya fuskanci tashe tashen wasu bama bamai a kusa da ofishin jakadancin kasar Amurka da biritaniya to amma bayanai sun shaidar da cewa babu wanda ya rasa ransa ko kuma ya jikkata.

Harv ila yau kuma an fuskanci wani tashin bom din a kudu maso gabashin birnin nin wanda sakamakon hakan yan iraqi uku suka samu muggan raunuka.

Bisa kuwa ci gaba tashe tashen hankula a kasar ta iraqi a yanzu haka ministan harkokin wajen kasar Hoshiyyar Zebari na can a birnin Brussels na kasar Belgium don neman kungiyyar ta cika alkawarin data daukarwa kasar na bawa jamian tsaron ta horo na musanman.

Zebari ya shaidawa yan jaridu cewa babu tantama a yanzu haka kasar ta iraqi na son irin wan nan taimako cikin gaggawa domin dakile aiyukan yan fadan sari ka noke dana kwanton buna dake gudanar da aikin assha a cikin kasar.

A waje daya kuma babban sakataren kungiyyar tsaron ta Nato Jaap Hoop ya tabbatar da cewa mambobin kasaashe 25 na kungiyar zasu duba irin wan nan koke na iraqin tare da daukar matakin daya dace a karshen watan nan da muke ciki.

A lokacin gudanar da wan nan musayar miyau a tsakanin kasashe mambobi na kungiyyar tsaron ta Nato babban sakataren ya shaidar da cewa kungiyyar za kuma ta duba bukatar da Zebari ya gabatar na neman a taimakwa kasar ta iraqi da kayan kariya na tsaro tare da bawa ofishin mdd dake kasar tsaro na musanman musanmamma bisa la,akari da cewa zabe na kara karatowa.

A daya hannun kuma a cewar kakakin mdd majalisar ta zabi Ashraf Jehangir Qazi dan kasar Pakistan ya zamo wakilin majalisar na musanman a kasar ta iraqi don cike gurbin Sergio Viera De Millo daya rugamu gidan gaskiya sakamakon tashin bom a babban ofishin mdd dake iraqi a shekara data gabata.

Kafin dai zabar Ashraf a wan nan mukami ya kasance jakadan kasar Pakistan a kasar Amurka.

A dai makon daya wuce ne kwamitin sulhu na mdd ya zartar da hukuncin bawa majalisar taka rawata musanman a iraqi dangane da lura da gudanar da zabe da sake gina kasar bayan yaki da kuma tabbatar da cewa bangarorin sharia na tafiya yadda ya kamata.

A wata sabuwa kuma har yanzu ana nan ana kai ruwa rana game da wa,adin da wadanda sukayi garkuwa da dan kasar Phillines din nan suka bawa gwamnatin kasar na janye dakarun su daga iraqi a ranar 20 ga watan nan da muke ciki.

Rahotanni dai sun rawaito tsohuwar jamiar kasar na fadin cewa gwamnati a shirye take ta janye dakarun sojin daga kasar to sai dai kuma bata fadi wani tsayayyen lokaci ba.

A yayin kuwa da ake wan nan kiki ka kann kasar Australia cewa tayi tana nan tana shirye shiryen kara yawan dakarun ta na tsaro a kasar ta iraqi don ci gaba da gudanar da aikin tabbatar da tsaro da kuma kare dukiyoyin alummar kasar.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin rikon kwarya ta iraqi ta dauki tsauraran matakai na yaki da yan taadda masu aikata miyagun aiyuka a iraqi a hannu daya kuma da yiwa wadfanda suka mika wuya ahuwa.

Ibrahim Sani.