1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI,.

SHUGABAN GWAMNATIN JAMUS MR SCHROEDER BAI YARDA DA YAKIN IRAQI BA; BLAIR NA BIRITANIYA YA MARA BAYA AN KAIWA IRAQI HARI.

default

Tabbatar da harkokin tsaro a iraqi har yanzu dai bai samu yadda ake zato ba duk kuwa da kokarin da gwamnatin rikon kwarya karkashin shugaban Iyad Alawi keyi a tun bayan darewar ta karagar mulki a farko farkon watan nan da muke ciki.

A misali kamar kullum a yau juma,a ma an fuskanci tashin wani bom a dai dai cincirindon dakarun sojin Amurka a tsakiyar birnin Bagadaza.

Ya zuwa yanzu dai babu wata majiya data tabbatar da salwantar rai ko kuma jikkata daga bangaren dakarun sojin na Amurka ko kuma fararen hula na yankin da abu ya faru a cikin sa.

A waje daya kuma wani dan sanda na kasar ta iraqi ya bakunci lahira babu shiri a can arewacin garin Kirkuk yayin da wasu yan fadan sari ka noke suka harbo masa gurneti.

A daya hannun kuma sakamakon wata arangama data wanzu a tsakanin dakarun sojin na Amurka da yan fadan kwanton bauna a garin falluja a yau juma,a bayanai sun shaidar da cewa mutane a kalla goma sha 13 suka samu raunuka iri daban daban to amma babu wanda ya rasa ransa daga bangarorin biyu.

A wata sabuwa kuma mutumin da ake zargi na shirya makarkashiyar kai hare haren kwanton bauna dana bama bamai a kasar ta iraqi wato, Abu musab Al zarqawi dake da alaka da kungiyyar Alqeeda a yanzu haka ya fito fili yayi ikirarin cewa kungiyyar sace tayi sanadiyyar mutuwar gwamnan garin Mosul a farko farkon makon nan da muke ciki.

Idan dai za a iya tunawa gwamna Osama Kashoula ya rasa ransa ne tare da wasu dogarawan sa biyu a ranar larabar data gabata lokacin da yake mota a kann hanyar sa ta zuwa Bagadaza daga garin na Mosul.

Ba a da bayan wan nan kuka kungiyyar ta Al zarqawi ta kuma ikirarin cewa tana da hannu a cikin ire iren hare haren bama baman da ake fuskanta a cikin kasar ta iraqi wanda hakan yake sanadiyyar mutuwar dakarun sojin hadin gwiwa da kuma wasu tasiraru fararemn hula.

Bisa kuwa ire iren wadan nan abubuwa da suke faruwa a jiya alhamis ne faraministan kasar ta iraqi Iyad Alawi ya bayar da sanarwar kafa wata hukuma ta musanman da zata dinga yaki da aiyukan yan taadda da kuma taaddanci a fadin kasar ta iraqi baki daya.

Wan nan sabuwar hukuma a cewar Iyad Alawi zata kasance hukumar da zata fatattaki hauren baki dake ingiza wutar rikice rikice a kasar ta iraqi izuwa kasashen su na asali.

A wata sabuwa kuma a yau juma a ne dakarun sojin kasar phillipines suka fara janyewa daga kasar ta iraqi izuwa gida.

Daukar wan nan mataki kuwa ya biyo bayan wa,adin da aka basu ne da yake karewa a yau juma,a nasu fice daga kasar ko kuma a aike da dan kasar daya wato Filipino lahira ta hanyar fille masa kai.

A don haka a cewar bayanai da suka iso mana kasar ta bayar da sanarwar janye tawagar sojin dake bayar da tallafin gaggawa daga kasar a hannu daya kuma da jamian sojin ta guda 10. Ya zuwa yanzu sojojin kasar 32 ne kawai suka rage a kasar ta iraqi.

Rahotanni dai sun nunar da cewa matukar mahukuntan kasar ta Phillipines basu dauki wan nan mataki ba to babu shakka wadanda sukayi garkuwa da Filipino zasu hallaka shi.

Ibrahim sani.