1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

.: HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

SHUGAGABAN KASAR IRAQ DA MAI MASAUKIN BAKIN SA SHUGABAN GWAMNATIN JAMUS.

default

Har yanzu dai kura bata natsa ba dangane daci gaba da rashin zaman lafiya dake faruwa a kasar Iraqi.Domin kuwa koda a yau juma a bayanai da suka iso mana sun shaidar da cewa dakarun sojin Amurka sunyi ruwan harsashai a garin falluja dai dai da inda suke zargin cewa yan fadan sari ka noke dana kwanton bauna na boye a ciki.

A cewar wadanda suka ganewa idon su yadda wan nan al,amari ya faru sun rawaito cewa mutum daya ya rasa ransa wasu kuma biyu sun jikkata.

Bayanai dai sun shaidar da cewa bayan asarar rayukan daruruwan mutanen yankin na Falluja a makonni kadan daya gabata sojojin na Amurka sun fice daga garin ne a watan mayu tare da danga harkokin tsaron garin ga hannun yan sanda.

To amma duk da haka a cewar rahotanni da suka iso mana har yanzu ba a rabu da bukar ba domin kuwa daga wancan lokaci kawo yanzu har yanzu yan fadan sari ka noke dana kwanton bauna na nan nacin karen su babu babbaka.

Bugu da kari rahotanni sun tabbaqtar da cewa daga wancan lokaci izuwa yanzu babu ranar Allah da zata zo ta wuce ba ayi dauki ba dadi ba a tsakanin dakarun Amurka da kuma magoya bayan Muqtadar sadr,wanda hakan ne yake kawo irin asarar rayukan da ake a kullum ranar Allah taala.

A kuwa ta bakin sojin Amurka,Cewa sukayi mutanen garin na Falluja nada alaka ta kusa da dan taaddan nan wato Abu musab Al zarqawi.

Tun a can baya dai Sojojin na Amurka sun shaidar da cewa Abu musab wanda dan asalin kasar Jordan ne na daya daga cikin irin mutanen dake shirya makarkashiyar kawo musu hare hare a hannu daya kuma da irin bama bamai da ake dasa musu a kann tituna.

A wata sabuwa kuma masana kann Al,amurran makamai na Amurka zasu gabatar da rahoton su na karshe kann mallakar makaman nukiliya da aka zargi Saddam Hussain na iraqi da Mallaka ko kuma akasin haka.

A cikin shafinta na farko a yau juma,a jaridar Guardian cewa tayi sifetocin da Amurka ta nada game da wan nan Aiki zasu gabatar da rahoton nasu ne nan na makonni biyu masu zuwa hakan shi zai share fagen tantance irin zarge zargen da akewa Saddam Husasain a can baya kafin afka masa da yaki.

Wadan sifetoci da yawan su ya kai a kalla dubu daya sun isa kasar ta Iraqi ne a watan yuli na shekara ta 2003,wanda yayi daidai da watanni hudu bayan kammala yaki.

A can baya dai wan nan kwamiti ya taba gabatar da kwarya kwaryan rahoton sa inda ya nunar da cewa bayan bincike da jamian suka gudanar babu wani makami na nukiliya da suka gano bisa irin hasashe ko kuma zargi da akewa Saddam Hussain na mallakar muggan makamai masu guba.

Madugun wan nan kwamiti wato David Kay ya kara jaddada wan nan mataki nasu kafin yayi murabus daga shugasbancin wan nan tawaga watanni uku bayan fara wan nan gagarumin aikin.

Fitar da wan nan rahoto na karshe a cewar bayanai da suka iso mana babu shakka zai saka shugaba Tony Blair da Shugaba Bush a cikin wani hali na tsaka mai wuya bisa la,akari da cewa zabubbuka na nabn tafe a kasashen nasu a hannu daya kuma da irin tsaiwa ta daka da sukayi a kann matakin cewa Saddam Hussain nada wadan nan makamai a boye.

Ibrahim Sani.