HALIN DA AKE CIKI A IRAQi. | Siyasa | DW | 17.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQi.

JAMIAN DAKARUN SOJIN MUQTADAR AL SADR

default

Babu shakka babu koja a yanzu za a iya cewa kasar Iraqi ta koma wani dandali na tashe tashen hankula da kuma rigingimu,wanda a kullum Ranar Allah ta ala sai anyi asarar rayukan mutane da daman gaske.

A misali a yau juma a kamar kullum mutane biyar ne suka ce ga garin ku nan wasu kuma talatin suka jikkata sakamakon tashin wasu bama bamai a cikin wata karamar mota a tsakiyar birnin Bagadaza.

Rahotannin da suka iso mana sun shaidar da cewa wani dan kunar bakin wake ne da ba a san ko wane ne ba ya ajiye motar dauke da bama baman a cikin tsakiyar motocin yan sanda dake birnin Na bagadaza.

Bugu da kari bayanan sun kuma shaidar da cewa tashin bama baman yayi asarar wasu motocin yan sanda guda biyu wasu kuma biyar sun lalace kwarai matuka.

Maikatar lafiya ta birnin na Bagadaza ta tabbatar da cewa wadanda suka jikkatan suna cikin mawuyacin hali sakamakon buguwa da sukayi. Wadan da kuwa suka rasu,da yawa daga cikin su naman su cike da jina sai yawo yake a kann titin da abin da wan nan al,amari ya faru a cikin sa.

Jim kadan dai bayan faruwar wan nan al,amari yan sanda da dakarun sojin Amurka suka rufe hanyar da abin ya faru don gudanar da aikin agajin gaggawa ga wadan da abin ya rutsa dasu.

Idan dai za a iya tunawa,a ranar talatar data gabata wani bom ya tashi a kusa da wani ofishin yan sanda a birnin na bagadaza ,wanda hakan yayi ajalin mutuwar mutane a kalla 49,ban da wasu da dama da suka jikkata.

A wata sabuwa kuma a yayin da ake cikin wan nan hali bayanai daga Amurka sun shaidar da cewa daga ko wane lokaci a nan gaba sifetocin bincike na Amurka a iraqi ka iya fitar da rahoton su dangane da mallakar makaman nukiliya.

A cewar wasu bayanai na wajen fage da suka iso mana sun shaidar da cewa wan nan rahoto mai shafi dubu daya da dari biyar zai share hanyar zargi da aka dade da yiwa gwamnatin ta Iraqi game da mallakar makamin nukiliya wanda hakan ne ya haifar aka gabatar da yaki a kanta.

A cewar bayanan akwai alamun cewa rahoton ya tabbatar da cewa kasar ta iraqi bata da wadan nan makasmai da aske zargin ta da kerawa to sai dai kuma akwai alamun cewa Saddam hussain yayi kokarin ci gaba da daukar hanyar kera su a lokacin yana gadon sarauta.

A Kuwa ta bakin madugun siofetocin Mr Charles Duelfer cewa yayi kasar ta iraqi bata da cikakkun dakin bincike na kayan kimiyya da fusaha da zai basu damar sarrafa sanadarin yin makamin na nukiliya.

Hakan a cewar rahoton na nuni a fili da cewa kasar ta iraqi bata da sanin makamar kera makamin na nukiliya.

A waje daya kuma idan An iya tunawa kasar Amurka da kawayen ta sun kai wan nan yakin ne kann kasar ta iraqi bisa hujjar cewa tana kokarin kera makamin nukiliya na kare dangi yanzu kuma alamu na nuni da cewa kasar ta iraqi bata da wadan nan makamai da ake zargin ta da kerawa ko kuma mallaka.

Ana dai sa ran cewa nan da yan makonni kadan masu zuwa za a fito da cikakken bayanin dake kunshe a cikin wan nan rahoto,don a yada duniya ta sani.

Ibrahim Sani.