1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

sojan amurka a garin samarra na kasar iraqi lokacin gudanar da hare haren su.

default

Idan daddawa nada wari akace bera ma nada sata. Kamar kullum a yau juma a dakarun sojin kasar Amurka da yan sandan kasar sun gudanar da wani mummunan har mai munin gaske ga yan fadan sari ka noke da kuma na kwanton bauna a garin samarra na kasar ta iraqi.

Wan nan hari bisa rahotannin da suka iso mana yayi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 90 banda kuma wasu 100 da suka jikkata.

A cewar babban likitan asibitin samarra Dr Khalid Ahmed,banda wadan nan da suka rasa rayukan nasu,sojan Amurka daya ya rasa ransa wasu kuma hudu sun jikkata.

Garin dai na samarra a cewar rahotanni ya kasance gari da yan fadan sari ka noke dana kwanton bauna suka mayar babban sansanin su a kasar ta iraqi.

Wan nan dai hari bisa bayanan da suka iso mana ya biyo bayan yunkurin da dakarun mamayen keyi ne na ganin sun kwato garuruwan Falluja da samarra da kuma ramadi daga hannun yan fadan sari ka noken da suka mayar da wadan nan garuruwan sansanin su da suke shirya miyagun aiyuka.

Bugu da kari bayanai sun shaidar da cewa dakarun mamayen na gudanar da ire iren wadan nan hare hare ne don ganin cewa an samu kwanciyar zaman lafiya a kasar kafin zuwan lokacin gudanar da zaben gama gari da aka shirya yi a watan janairun sabuwar shekara.

A cewar wani mazauni a garin na Samarra,sunyi kwanan zaune a daren jiya juma a sakamakon irin ruwan bama baman da sojojin mamayen suka dinga gudanarwa.

Mazaunin mai suna Said Mohd dan shekaru 33 yaci gaba da cewa da yawa mazauna garin sun rufawa gidajen su tankuna don kare saukar harsashai a cikin gidajen nasu ko kuma makamancin hakan.

A dai cikin yan makonni da dama da suka wuce bayanai sun shaidar da cewa yan kungiyar Abu Musab Al zarqawi nada hannu dumu dumu a cikin hare hare da ake kaiwa dakarun sojin na Amurka a kasar ta Iraqi a hannu daya kuma da sanadiyyar tashe tashen bama baman da kasar take fuskanta.

Wan nan nan nema ya haifar dakarun sojin na Amurka suka rusa wani gida a can garin Falluja da akace na Abu musab Al zarqawi din ne.

Ya zuwa yanzu dai mahukuntan kasar ta iraqi sun kudiri aniyar daukan tsauraran matakai na tsaro don ganin zaman lafiya ya wanzu a fadin kasar baki daya,musanmamma kafin lokacin zuwan zabe.

A waje daya kuma faraministan kasar ta Iraqi Iyad alawi ya kara nanata matakin gwamnatin sa naci gaba da gudanar da shirye shiryen zaben watan Janairun sabuwar shekara koda kuwa harkokin tsaro a kasar basu inganta ba.

A waje daya kuma da yawa daga cikin masu sharhin siyasa na yankin Gabas ta tsakiya na ganin cewa gudanar da zabe a kasar ta iraqi a halin da ake ciki yanzu na rashin kyakkyawabn tsaro ka iya haifar da dan da bashi a ido a nan gaba.

Bisa hakan a ganin su kamata yayi ace an samu kwanciyyar hankali as fadin kasar baki daya kafin gudanar da zabe a kasar.

Ibrahim Sani.