1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

October 8, 2004

TANKUNAN YAKIN AMURKA A IRAQI

https://p.dw.com/p/Bvfo
Hoto: AP

Kamar ko wane lokaci a safiyar yau juma a dakarun sojin Amurka sun kai wasu sabbin hare haren bama bamai a garin Falluja.

Wan nan hari bisa rahotannin da suka iso mana yayi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 12 wasu kuma da daman gaske suka jikkata.

Wan nan dai hari a cewar bayanan da suka iso mana ,an kaishi ne a cikin taron aure da ake a garin na Falluja,wanda hakan ya haifar ango da amaryar suma na daga cikin mutanen da suka sheka izuwa lahirar.

A daya wajen ,kuma dakarun mamayen sun shaidar da cewa sun kai wan nan harin ne da niyyar samun magoya bayan kungiyyar Alqeeda ta Abu musab Al zarqawi dake boye a wasu yankuna na garin na Falluja.

Bugu da kari dakarun mamayen sun kuma nunar da cewa wan nan hari zai rage karfin kungiyyar ta Al zarqawi na gudanar da ire iren shirye shiryen ta na taaddanci a fadin kasar ta iraqi baki daya.

A cewar wata sanarwa da dakarun sojin na Amurka suka fitar ta shaidar da cewa akwai kwararan bayanai dake nuni a fili na mambobin kungiyyar ta Alqeeda da Abu musab Alzarqawi kewa jagoranci na gudanar da tarurruka daban daban a wani gida dake cikin garin na Falluja.

Bisa hakan daga wan nan lokaci izuwa yanzu dakarun mamayen suka dauki aniyar kai hare haren a yankunan da wadan nan mutane suke.

Ya zuwa yanzu dai wadan nan gurare dake cikin garin na Falluja tuni sojin na Amurka suka bayar da sanarwar daina zirga zirga a wadan nan yankuna a wani mataki na tabbatar da harkokin tsaro a garin na Falluja.

Kungiyyar ta Abu musab Al zarqawi dai na daga cikin ire iren kungiyoyin dake ikirarin kai hare hare a fadin kasar ta iraqi baki daya,wanda hakan ne ma ya haifar kasar Amurka ta saka ladan tsabar kudi har dalar amurka miliyan 25 ga dukkannin mutumin daya gano inda Abu musab Al zarqawi din yake da buya.

A wata sabuwa kuma gidan talabijin din Abu Dabi ya rawaito cewa wasu magoya bayan kungiyyar ta Abu musab Alzarqawi ta halaka dan kasar Biritaniya din nan wato Ken Bigly da akayi garkuwa dashi a yan makonnin baya da suka gabata.

Rahotanni dai sun nunar da cewa yan kungiyyar ta Al zarqawi ta gabatar da wan nan danyxan aikin ne bisa kin cuika bukatar da suka gabatar na sako dukkannin matan da ake tsare dasu a cikin gidan yarin kasar ta iraqi.

A daya hannun kuma bisa rashin tsaro dake ci gaba da wanzuwa a kasar ta iraqi,kwamandan askarawan Amurka a iraqi janaral David Petraeus ya sadu da jamian kungiyyar tsaro ta Nato 25 don neman kungiyyar ta kawo dauki a kasar ta iraqi game da tura sojojin kiyaye zaman lafiya.

Wadan nan sojoji a cewar kwamandan askarawan na Amurka zasu ja ragamar bawa jamian tsaron kasar ta iraqi horo ne na musanman a wajen kasar ba a cikin kasar ta ikraqi ba.

Ana dai sa ran cewa za a cimma matsaya guda a tsakanin wadan nan jamiai dangane da wan nan bukata ta kwamandan askarawan na Amurka daga yanzu izuwa daren gobe asabar.

Ibrahim sani.