HALIN DA AKE CIKI A IRAQI. | Siyasa | DW | 12.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HALIN DA AKE CIKI A IRAQI.

wata yar iraqi na jimamin mutuwar danta bayan tashin wani bom a ikraqi.

default

Har yanzu dai harkokin rashin tsaro a iraqi na nan tamkar jiya a yau. A misali bayanan da suka iso mana sun nunar da cewa dakarun sojin Amurka sun kai wasu hare hare da kana nan jiragen sama a wasu gurare da yan fadan sari ka noke ke boye a garin Falluja.

Rahotanni sun nunar da cewa sakamakon wan nan hari mutane a kalla guda hudu ne suka rasa rayukan su wasu kuma da dama suka jikkata.

Bugu da kari harin ya kuma yi sanadiyyar lalata gidajen kwana na mutanen yankin guda a kalla biyu.

Gamsassun bayanai dai na nuni da cewa wan nan mummunan hari da dakaerun sojin na amurka suka kai a gartion na Falluja nada nasaba da bayanan da suka samu ne na cewa yan kungiyyar Abu musab Al zarqawi na boye a wasu gurare a cikin garin na Falluja.

Daga kuma wadan nan gurare ne wadan nan mutane a cewar bayanan da suka iso mana suke ashirya ire iren makircin kai hare haren kwanton bauna dana sari ka noke kann dakarun mamayen dake cikin kasar ta iraqi.

A waje daya kuma,wata sanarwa data fito daga yan dafan sario ka noken kasar ta iraqi ta tabbatar da fillewa dan kasar turkiyyan nan kai tare da mai masa fassara dan kasar ta iraqi.

Sanarwar taci gaba da cewa an aike da wadan nan mutane biyu izuwa lahira ne bayan da aka tabbatar da cewa suna rufawa dakarun sojin Amurka baya game da irin hare haren da suke kaiwa yan fadan sari ka noken kasar ta iraqi.

A daya hannun kuma ya zuwa yanzu magoya bayan Muqtadar Al Sadr na nan naci gaba da mika makaman su hannun dakarun sojin Amurka bisa yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin bangarorin biyu game da tsagaitawa da bude wuta don samumn wanzuwar zaman lafiya a fadin kasar baki daya.

Hausawa dai kance ana wata sai ga wata a yayin da ake cikin wan nan hali na kawo karshen irin balahirar dake faruwa a tsaklanin wadan nan bangarori na sama a dai dai lokacin ne kuma dakarun sojin na Amurka suka kai wani sumame don cafke wasu masu tsattsauran raayi a cikin wasu7 masallatai dake garin Ramadi.

Sakamakon wan nan dauki ba dadi bayanan sun shaidar da cewa mutane hudu ne suka rasa rayukan su wasu kuma da yawa suka jikkata.

Rahotanni dai sun nunar da cewa daga cikin wadan da aka cafken har da wani babban jamii dake daya daga cikin manya manyan malamai da ake gani da gashi a kasar ta iraqi.

A cewar wani babban hafsan sojin Amurka sun kai wan nan sumamen ne a masallatai guda bakwai bisa dalilin cewa suna bawa yan taadda mafaka a hannu daya kuma da zamowa dakin taro don shirya irin hare haren da za a kaiwa sojojin na Amurka a fadin kasar ta iraqi baki daya.

A yayin kuwa da ake cikin wan nan yanayi a wasu yankunan kasar ta iraqi a can kuma garin kirkuk,daya daga cikin shugabannin kabilar kurdawa wato Massoud Barzani cewa yayi kabilar su a shirye take ta kwatowa kanta yanci na sarrafa irin albarkatun man da ake hakowa a yankin a maimakon ci gaba da raja a kann gwamnatin rikon kwarya karkashin Mr Iyad Alawi.

Shugaban kurdawan dai ya fadi hakan ne jim kadan bayan ganawar sa da shugabannin kasar turkiyya a can birnin Ankara a yau talata.

Idan dai za a iya tunawa yankin na Kirkuk na daga cikin manya manyan guraren da ake hakar man fetur a cikin kasar ta iraqi.

Ibrahim Sani.